Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-21 15:04:39    
Dalibai masu dalibta na Korea ta Kudu na sha'awar zama masu aikin sa kai na taron wasannin Olympic na Beijing

cri
Yanzu ana share fage ga taron wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008 bisa matakai yadda ya kamata. Daukar masu aikin sa kai wani muhimmin bangare ne na ayyukan shirya wannan muhimmin taron wasanni. Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi shirin daukar masu aikin sa kai domin gasanni daga ketare tun daga kwannaki 10 na karshe na wannan wata, a hukunce ne zai karbi rajistar da mutanen ketare suka yi. A cikin Jami'ar horar da malaman koyarwa ta Beijing, dalibai masu dalibta na kasashen waje da yawa sun nuna sha'awa sosai kan taron wasannin Olympic na Beijing mai zuwa, suna fatan za su yi kallon wannan kasaitaccen taron wasanni a idanunsu, sa'an nan kuma, suna fatan za su ba da gudummowarsu. A kwanan baya, wakilinmu ya yi zantawa da dabilai masu dalibta na kasar Korea ta Kudu.

Malam Kim Dae Su, wani saurayi ne mai shekaru 27 da haihuwa, ya taba aiki a cikin wani kamfani na kasar Korea ta Kudu kafin ya zo nan Beijing don yin karatu. Ya yi watanni 6 yana nan kasar Sin, ya bayyana cewa, yanzu a ko wace ranar da yake zama a Beijing, yana jin cewa, taron wasannin Olympic yana zuwa, wasu daga cikin abokansa na kasar Sin sun yi rajista don zama masu aikin sa kai a shekara ta 2008, shi ya sa yana alla-allar yin rajista. Ko da yake a lokacin da wakilinmu yake zantawa da shi, ba a fara daukar masu aikin sa kai daga ketare ba tukuna, amma Kim ya riga ya tsara shiri gaba daya kan ayyukan da zai yi bayan da ya zama masu aikin sa kai, ya ce,'Ina fatan yin ayyuka iri daban daban bisa karfina, amma in na zama mai aikin sa kai, ina son nuna hanya a cikin filayen wasa, in gaya wa mutane gasannin da za a yi, irin wadannan ayyuka na da sha'awa sosai.'

Malam Lee Sang Yoon, wani abokin karatun Kim, shi ma mutun ne mai sha'awar kasar Sin sosai. ya kasa boye farin cikinsa a lokacin yake magana kan taron wasannin Olympic na Beijing. Ya ce,'Ina mai da hankalina sosai kan taron wasannin Olympic na Beijing, saboda kasarmu ta taba shirya taron wasannin Olympic a shekara ta 1988, a lokacin can ina mataki na 3 a makarantar firamare. Bayan da kasarmu ta yi taron wasannin Olympic a birnin Seoul, ta sami saurin ci gaban zaman al'umma da tattalin arziki ainun, ta jawo hankulan kasashen duniya a sakamakon shirya irin wannan kasaitaccen taron wasanni na matsayin duniya, shi ya sa na yi imanin cewa, shirya taron wasannin Olympic a nan Beijing a shekara ta 2008 zai sanya kasar Sin ta kara jawo hankulan sauran kasashe, sa'an nan kuma, zai sa mata kaimi da ta kara samun saurin bunkasuwar tattalin arziki kamar yadda kasarmu ta yi.'

Malam Li ya kara da cewa, yanzu yana kokarin koyon Sinnanci, don neman zama mai aikin sa kai domin taron wasannin Olympic na Beijing a shekara ta 2008. Ban da taron wasannin Olympic na Beijing, malam Lee yana son ya ba da hidima ga birnin Beijing, ya ba da shawara kan raya birnin nan, wato ya fi kyau a kara shimfida hanyoyin jiragen kasa a karkashin kasa, ta haka za a iya isa wurare da yawa a Beijing cikin jiragen kasa a karkashin kasa.

Wani abokinsa malam Oh Se Won ya riga ya yi shekaru fiye da 2 yana koyon Sinnanci a kasar Sin, yanzu ya iya magana da Sinnanci sosai da sosai, shi ma ya mai da hankalinsa kan labarun da suka shafi masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympic na Beijing. Yana ganin cewa, yin ayyukan sa kai a gun taron wasannin Olympic na Beijing zai bai wa dalibai masu dalibta na kasashen waje taimako wajen samun aikin yi a nan gaba. Saboda taron wasannin Olympic wani wuri ne da ya iya jarraba kwarewar aiki ta matasa, don haka taron wasannin Olympic wata dama ce a gare shi. Ya ce,'Ina matukar fatan zama mai aikin sa kai a gun taron wasannin Olympic na Beijing. Wannan zai koyar mini wasu fasahohi a fannin harkokin zaman al'umma, wadanda za su ba ni taimako da yawa. Musamman ma a lokacin da nake neman aikin yi a Korea ta Kudu, an fi dora muhimmanci kan kwararrun da suka kware a kasarmu.'

Wani dalibi daban na Korea ta Kudu mai suna Choi Jin Young, da ke karatu a kasar Sin, yana son kasar Sin sosai. Ya kuma bayyana fatansa na zama mai aikin sa kai. Ya bayyana cewa, saboda ya taba yin aikin fassarawa a da, ko da yake kwarewarsa ta koma baya kadan a yanzu, amma zai iya kyautata kansa, zai iya kyautata Sinancinsa a shekara mai zuwa, saboda haka, tabbas ne zai iya taimaka wa saura a shekara mai zuwa.(Tasallah)