Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-21 15:04:39    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(15/03-21/03)

cri

Ran 14 ga wata, shugaba Jin Dapeng na hukumar kiwon lafiya ta birnin Beijing ya ce, birnin Beijing zai tabbatar wa jama'a koshin lafiya a lokacin da ake yin taron wasannin Olympics a nan Beijing a shekara ta 2008. Mr. Jin ya kara da cewa, birnin Beijing ya riga ya tabbatar da matsalolin da yawansu ya kai 45 kuma mai yiyuwa ne za su kawo illa ga taron wasannin Olympics da na nakasassu a shekara ta 2008. Ya kuma yi nazarin yiyuwar aukuwar wadannan matsaloli da hadarurrukansu. Wadannan matsaloli 45 suna kunshe da hadarurrukan annobar ciwace-ciwace da ingancin abinci da na ruwan sha da dai hadarurrukan jama'a da mai yiyuwa ne za su auku a sakamakon yaduwar kwayoyin cututtuka.

Ran 16 ga wata, a babban zaurenta da ke birnin Zurich, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta gabatar da sabon jerin sunayen kungiyoyin wasan kwallon kafa na mata na kasashen duniya. Kasar Amurka ta zama ta farko, kasar Sin kuwa ta yi kasa ta zama ta 11 a maimakon ta 9 a da. A cikin dukan kungiyoyi 142 na wasan kwallon kafa na mata a duk duniya da ke cikin wannan jerin sunaye, kasashen Amurka da Jamus da Norway da Sweden da Korea ta Arewa da Denmark da Faransa da Brazil da Japan da kuma Canada sun zama na farko zuwa na 10.


1 2