Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-21 15:03:36    
Wani mai aikin fasaha na kasar Sin da ke zama a kasar Jamus mai suna Liu Yonggang

cri

Kalmomin harshen Sinanci da na kananan kabilu na kasar Sin su ne muhimman abubuwan da ke cikin al'adun kasar Sin, kuma su ne almomin da ke wakilci al'adun gargajiyar kasar Sin. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, wasu masu aikin fasaha na kasar Sin na zamanin yau suna ta kara yin amfani da samfurorin kalmomin harshen Sinanci don sassaka mutum mutumi ko yin zane-zane da dai sauransu. Daga cikinsu, Mr Liu Yonggang da ke zama a kasar Jamus ya fi sauransu samun sakamako.

Kwanan baya, gidan baje kolin kayayyakin fasaha na kasar Sin ya yi nunin abubuwan da Mr Liu Yonggang ya sassaka da ke da lakabi haka: "Kalmomin harshen Sinanci da ke tsayawa tsaye cif" , daga ciki, da akwai wani kashin da ke cikin babban rukunin mutum mutumin da Mr Liu Yonggang ya sassaka ta hanyar yin amfani da duwatsu, tsayinsu ya kai mita uku ko fiye, in an hango su daga nesa, ana iya tsinkaya cewa, a tsakanin sararin samaniya mai launin shudi da ciyayi mai launin kore shar, ana iya gano abubuwa tamkar yadda mutane biyu suke rungume da juna, amma in aka mai da hankali sosai wajen duddubawa, sai ana iya gano cewa, kowane mutum mutumin da aka sassaka kalma ce da aka yi da ke tsayawa tsaye cif . Mr Liu Yonggang ya bayyana cewa, wadannan sifofin kalmomi da na yi daga kalmomi ne da aka rubuta a kan kasusuwan naman daji da na kunkuru na zamanin da na kasar Sin tare da kalmomin harshen Mongoliya da kalmomin harshen Basiba wadanda aka yi amfani da su ne a daular Yuan na karni na 13 a kasar Sin

A kasar Sin, ba a taba samun masu aikin fasaha da suka yi amfani da manyan duwatsu da yawa don mayar da kalmomin harshen kasar Sin a tsaye suke yi.Mr Liu Yonggang ya gaya wa manema labaru cewa, da na sauka kasashen waje, na je kallon nune-nunen da aka shirya da yawa, a kai a kai ne na ji cewa, dukkan abubuwan da na taba koyo a jami'ar gida da ta kasashen waje ban iya rike da su ba, su ne abubuwan da na koyo da kuma na maimaita su daga wajen sauran mutane, ba nawa ba ne, shi ya sa na ji cewa, dole ne ina da tushena, tushen din nan shi ne al'adun gargajiyar kasar mahaifa. Ina son kalmomin harshen Sinanci, shi ya sa na soma nazari kan kalmomin harshe na matakai daban daban na tarihi.

A shekaru 90 na karnin da ya shige, Mr Liu Yonggang ya tafi kasar Jamus don yin karatu, ya bayyana cewa, duk domin cim ma burin da ya yi tun lokacin da yake karami. Ya bayyana cewa, na taba je kallon wani nunin kayayyakin kasar Jamus da aka shirya a birnin Beijing, na ji ina kaunarsa sosai da sosai, shi ya sa ina da niyyar kai ziyara a wannan kasar wato kasar Jamus don dudduba kasar.

Kai, duk tsawon ziyarar nan ya kai shekaru goma ke nan, ba a samu labarinsa ba a kasar Sin, amma da ya koma gida ya shirya nuninsa na kansa, kai, aka yi tattaunawa sosai a kan abubuwan da ya yi , mutane sun yi mamaki sosai a kan rukunin mutum mutumi da ya sassaka da zane-zanen da ya yi, Mr Liu Yonggang ya hada da fasahohin kasar Sin da na kasar Jamus, malamin Liu Yonggang wato shehun malami na jami'ar koyar da fasahohi ta tsakiya ta kasar Sin Mr Wen Leipeng ya bayyana cewa, tare da himmarsa sosai ne ya hada da fasahohi iri daban daban na kasashen gabas da na yamma wajen yin zane-zane da sassaka mutum mutumi da rubuce-rubuce , ya cika kwarin da ke tsakanin fasahohin zamanin aru aru da na yanzu.

Daga shekarar 1999, Mr Liu Yonggang ya soma aikin sassakar babban rukunin mutum mutumi da ke da lakabi "rungume" ta hanyar yin amfani da sinadarin kalmomin harshen Sinanci na gargajiya, Mr Liu ya dora wa irin wadannan kalmomin da ke tsayawa kaunarsa sosai. Ya ce, da akwai kauna a cikin zuciyar mutane, to mutane za su iya rungume wa juna, yana fatan ana rungume da duniya ta hanyar kaunarsa, kuma yana son kaunar tana rungume da duk duniya.(Halima)