Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-20 16:07:42    
Ina son in zama manzon musamman na yin ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, in ji wani manaja

cri
Bisa albarkacin kasa samun bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Kenya ne, yawan masu yawon shakatawa na kasar Sin sun tafi kasar Kenya don yin ziyara sai kara yawa suke yi a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, daga cikinsu, mutane da yawa sun cim ma burinsu na kai ziyara a makekiyyar makiyayya ta Afrika ta hanyar kamfanin yawon shakatawa na kasar Sin da ke kasar Kenya, yanzu ga hirar da ke tsakanin wakilan gidan rediyo kasar Sin da babban manajan kamfanin Mr Zhang Yuanxiang .

wakilinmu ya yi wa manajan tambaya cewa, Mr Zhang, kai ne wane irin mutumi?

Mr Zhang ya yi murmushi ya amsa cewa, ni ne dan kasuwa ne kawai, amma ban yi ayyuka sosai a cikin harkokin kasuwanci ba.

A shekarar 1999, Mr Zhang ya sauka kasar Kenya daga wuri mai nisa sosai wato kasar Sin, kuma ya yi rajista a birnin Nairobi na kasar Kenya don kafa kamfanin yawon shakatawa. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bisa kokarin da ya yi tare da ma'aiakatan kamfaninsa ne, sha'aninsa ya sami bunkasuwa sosai. Amma a lokacin da kamfanin ya sami bunkasuwa da sauri a kowace rana, da wuya ana iya ganin Mr Zhang Yuanxiang a cikin kamfaninsa, kai a hakika dai ne, yana kan kai da kawowa ta hanyar jiragen sama daga kasar Sin zuwa kasar Kenya, yana mai da hankali sosai ga yin ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasar Kenya. Lokacin da ya tabo magana a kan burin farko da ya yi na yin ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasar Kenya, ya bayyana cewa, a lokacin farko, ya canja aikinsa na yin ma'amalar al'adu ne duk domin sa kaimi ga kara samun ci gaban harkokin kamfanin yawon shakatawa, ya ce, a ganina, ko shakka babu, irin ma'amalar al'adu ta iya kara raya aikin yawon shakatawa da kuma kara wa mutanen kasar Sin fahimtar kasashen Afrika da kuma kawo wa mutanen kasar Sin da yawa da suke ganin kasashen Afrika da idannunsu na kansu tare da sa kaimi ga raya aikin yawon shakatawa. A gaskiya dai, ayyukan da na yi na yin ma'amalar al'adu sun tsawaita ayyukan yawon shakatawa gare ni kawai.

Amma, bisa albarkacin kara zurfafa ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasar Kenya, Mr Zhang Yuanxiang ya fahimta cewa, yana kaunar sabon aikin nan a kai a kai. Musamman ma a lokacin da ya gano cewa, jama'ar kasashen biyu wato Sin da Kenya ba su fahimci junasu sosai ba, sai ya gane cewa, ya sami sarari mai fadi na samar da gudumuwarsa. Ya bayyana cewa, Bisa alamar tunawa da mutanen kasar Kenya suke yi wa mutanen kasar Sin, yawancinsu suna hira a kan abubuwa dangane da kasar Sin ta hanyar sinimar karate ta kasar Sin kawai, amma sinimar ba su iya bayyana abubuwan kasar Sin daga dukkan fannoni ba, musamman ma wajen abubuwan al'adu. Kodayake mutanen kasar Kenya suna abuta da mutanen kasar Sin sosai, amma bai kamata ba a bayyana wannan a wajen zumunci kawai, ya kamata a wajen kara yin ma'amalar al'adu a tsakaninsu don mayar da huldar da ke tsakaninsu su zama huldar da ke tsakanin 'yanuwa na gaskiya.

Bisa burin nan ne, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, Mr Zhang Yuanxiang ya shirya aikace-aikace da yawa tamkar yadda nunin hotunan da wani mashahurin mai dauka hotuna na kasar Sin Mr Luo Hong ya yi a hukumar tsara fasalin muhalli na Majalisar dinkin Duniya da dai sauransu, sa'anan kuma ya bayyana wa mutanen kasar Sin makekiyyar makiyayya ta Afrika mai kyaun gani sosai ta hanyar littattafai da hotunan da aka dauka da internet da sauran hanyoyi, daga shekarar 2004, Mr Zhang ya kuma jagoranci 'yan wasan kasar Kenya guda biyar zuwa birnin Xiamen na kasar Sin don shiga gasar dogon gudu, wato gasar Maratshon ke nan. Ya gaya wa manema labaru cewa, in an kwatanta sa da dan kasuwa , ya fi son y0.a zama mai yin ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.(Halima)