Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-20 15:22:12    
Baligan da suke zama tare da yaransu sun fi yawan cin abinci mai mai

cri

Bisa wani rahoton nazari da kasar Amurka ta bayar a kwanan nan, an ce, baligan da suke zama tare da yara sun fi yawan cin abinci mai mai idan an kwatanta su da wadanda ba su yi zama tare da yara ba.

Manazarta na jami'ar Lowa da kuma kwalejin kiwon lafiya na jami'ar Michigan ta kasar Amurka sun gudanar da bincike ga baligai 6600 wadanda shekarunsu ya kai 17 zuwa 65 da haihuwa. Daga baya kuma sun gano cewa, baligan da suke zama tare da yara sun fi cin abinci mai mai da ya kai gram 4.9 a ko wace rana idan an kwatanta su da wadanda ba su yi zama tare da yara ba.

Kuma rahoton ya bayyana cewa, bambancin da ke tsakanin wannan bincike da wadanda aka gudanar da su a da shi ne, mutanen da suka shiga binciken sun zo daga kabilu dababan daban, kuma launin fatansu da kuma matsayinsu wajen tattalin arziki sun sha bamban. Ban da wannan kuma rahoton ya nuna cewa, a da manazarta su kan mai da hankali kan tasirin da baligai suka bayar ga yara wajen cin abinci kawai, amma sun yi watsi da rawar da yara suke taka ga baligai wajen cin abinci.

Bugu da kari kuma rahoton ya ce, samun kiba fiye da kima wani muhimmin dalili ne da ke haddasa ciwon zuciya, shi ya sa ya kamata baligan da ke zama tare da yara su fi dora muhimmanci kan abincin da suke ci.

Likita La Roche mai kula da wannan bincike ya bayyana cewa, dalilin da ya sa baligan da suke zama tare da yara su kan ci abinci mai mai masu yawa shi ne sabo da su kan samu matsin lamba daga zaman rayuwarsu, da kuma tasirin da tallace-tallace suke bayarwa wadanda ake yi don yara kawai. Ban da wannan kuma a kan kiyaye abincin da ake shiryawa don yara a gida, wadannan baligai su kan ci irin wannan abinci tare da yara.

Ban da wannan kuma likita La Roche ya ba da shawarar cewa, ya kamata baligan da ke zama tare da yara su yi iyakacin kokari wajen daina cin abinci mai mai. Haka kuma ya kamata su kara shan nono maras mai sosai, da kuma dafa abinci tare da man zaitun a maimakon man shanu ko na sauran dabbobi. Ban da wannan kuma bai kamata su ci abinci irin na fast food da pizza fiye da sau biyu a ko wane mako ba.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan sha'anin ilmi na kasar Sin. Yanzu dalibai mafi yawa da suke cikin yankunan da ke da wuyar zuwa a kasar Sin suna iya sauraron darusan da shahararrun malamai suke bayarwa ta tashar. Kuma dalibai masu fama da talauci suna iya samun bashin daga bakunan kasar Sin don karatu. Haka kuma daga shekarar da muke ciki, yaran da ke kauyukan kasar Sin suna iya shiga makarantun firamare da sakandare bayan da suka biya kudin littattafai kawai. Dukkan wadannan al'amuran da ke faruwa sun shaida cewa, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin tana mai da hankali kan tafiyar da ayyuka iri iri domin sa kaimi ga samun ilmi cikin daidaici. To, za mu yi muku bayani kan batun.(Kande)