Babban dutsen Yantai na nan ne a gabashin birnin Yantai, fadinsa ya kai misalin kadada 24, ruwan teku na kewayensa daga gefuna 3. An kafa wani ginshikin fitila mai nuna hanya a teku a kololuwarsa a shekara ta 1398 tare da wani gidan fitila mai nuna hanya a teku, wanda ya riga ya zama alama ga Yantai. A shekara ta 1979, an raya wannan babban dutse an mai da shi wurin shakatawa. Shi ya sa an soma yin masa gyare-gyare.
Bayan da aka yi kwaskwarima kan ofisoshin jakadu guda 17 na kasashen waje da ke kewayen wannan babban dutsen, hukumar birnin Yantai ta bude wadannan gine-gine da aka gina a shekara ta 1862 zuwa ta 1932 domin masu yawon shakatawa bude ido.
A shekara ta 1861, an tilasta wa gwamnatin daular zamanin Qing ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Tianjin, ta haka birnin Yantai ya bude tashar jirgin ruwa bisa yarjejeniyar, a shekara ta 1862, gwamnatin zamanin daular Qing ta kaddamar da ofishin aikin kwastam na farko nata wanda ke kula da harkokin arewacin kasar a birnin Yantai. Kasashen Birtaniya da Amurka da Faransa da Japan da Jamus da Rasha da Spain da Italiya da Netherlands da kuma Sweden sun shiga jeri na farko wajen gina ofisoshin kananan jakadunsu a Yantai.
An bude wasu dakunan ajiye kayayyakin gargajiya a cikin wadannan tsoffin gine-gine, kamar su gidan da wani karamin jakada ke zama a lokacin can, da dakin nune-nunen takardu da yarjejeniyoyin da aka dadale a lokacin can, da kuma wani dakin ajiye agogo.
An yi amfani da kudin Sin yuan miliyan 20 ko fiye wajen yin kwaskwarima kan dukan wadannan ofisoshin kananan jakadu. An kuma ci gaba da aiki na mataki na 2, wanda aka zuba kudin Sin yuan sama da miliyan 100. Dukan wadannan tsoffin gine-gine na da sigogi iri daban daban nasu. Ban da wannan kuma, an adana dakunan wasannin motsa jiki da kantuna da kamfanoni da gidajen waya yadda ya kamata, wadanda aka samu a kewayen babban dutsen. Har zuwa yanzu, masu yawon shakatawa suna iya wasan kwallon bowling a cikin dakin wasan kwallon bowling da 'yan kasar Birtaniya suka gina a shekara ta 1865. Ayyukan kwaskwarima sun kuma jawo hankulan kasashen Birtaniya da Amurka da Japan da kuma Faransa, wasu daga cikinsu sun yi sha'awar ba da tallafi.(Tasallah)
|