Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-19 17:48:45    
Takaitaccen bayani game da kabilar Jingpo

cri

Yawancin 'yan kabilar Jingpo suna zama a gundumomin Luxi da Ruili da Longchuan da Yingjiang da Lianghe da suke yankunan tsaunuka na shiyyar Dehong ta kabilun Dai da Jingpo mai cin gashin kanta ta lardin Yunnan. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Jingpo ya kai fiye da dubu 130. Suna amfani da yaren Jingpo da kalmomi da haruffan Jingpo.

'Yan kabilar Jingpo suna zama a yankunan da tsayinsu ya kai mita tsakanin 1500 da dubu 2 daga leburin teku. Ana jin dadin yanayin wadannan yankuna sosai, kuma ana da wadatattun gonaki. Amma domin manoma ba su da gonakinsu, suna cikin mawuyacin hali sosai. A shekarar 1953, gwamnatin kasar Sin ta kafa shiyyar Dehong ta kabilun Dai da Jingpo mai cin gashin kanta. 'Yan kabilar Jingpo sun fara samun ikon siyasa na mulkin kasar. Bugu da kari kuma, an kafa wasu matsakaitu da kananan masana'antun samar da wutar lantarki da na ban ruwa da sarrafa shinkafa da man girke da garin alkama a yankunan kabilar Jingpo. A waje daya kuma, an kafa asibitoci da dakunan jiyya da makarantun firamare a dukkan yankunan kabilar Jingpo da makarantun sakandare a kowace gundumar da 'yan kabilar Jingpo suke zama.

A ciki dogon loakcin da ya wuce, 'yan kabilar Jingpo sun kirkiro adabi da abubuwan fasahohin zane-zane da wakoki da raye-raye iri iri.

Bisa al'adar kabilar Jingpo, kowane saurayin kabilar yana iya auren mace daya. Amma a da wasu masu hannu da shuni suna kuma auren mata fiye da daya. A cikin kowane gidan kabilar, mahaifi shi ne mai gida. Idan wani gida ba shi da da namiji sai yarinya, lokacin da yarinya take yin bikin aure, ango zai kuma shiga gidan amariya, amma ango ba zai canja sunan kakanin-kananinsa ba.

Yawancin 'yan kabilar Jingpo suna cin shinkafa, amma wasu sun fi son cin masara. A da, kafin su ci abinci, a farko dai, sun pakitin shinkafa a cikin ganyen ayaba domin raba wa iyalai. Suna kuma shan ruwan da aka samu daga cikin tsaunuka da giyar da aka yi da shinkafa. Gidan 'yan kabilar Jingpo gida ne da yake kama da bukkar Hausawa da aka gina su da karan gora da busasshen ciyayi. Sai tsirarrun masu hannu da shuni ne suke da gidajen zamani. Irin wannan bukkar da 'yan kabilar Jingpo suke zama tana da benaye 2. A benen farko, ana kiwon dabbobi da tsuntsaye na gina, iyalai suna zama ne a bene na biyu. A kowadanne shekaru 7 ko 8, ana sake gina gidansa. Lokacin da ake gina gida, kauyawa suna taimakawa juna.

A da ,'yan kabilar Jingpo suna bin addininsu na gargajiya, amma a cikin shekaru da dama da suka wuce, wasu 'yan kabilar sun fara bin addinin Kirista.(Sanusi Chen)