Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-16 21:34:01    
Wani mashahurin mawallafin kasar Sin mai suna Chen Zhongshi

cri

Mr Chen Zhongshi ya yi zama a wani kauyen da ke arewa maso yammacin kasar Sin cikin dogon lokaci, ya sami wata lambar yabo mai matsayin koli da ake kira lambar yabo ta Mr Mao Dun wajen wallafa wani kaggagen labari mai suna Bailuyuan wanda ya bayyana zaman rayuwar manoma da sauyawar da aka samu a kauyukan kasar Sin.

Jama'a masu sauraro, abin da kuka ji dazun nan shi ne wata wakar gargajiyar shiyyar Bailuyuan da ke lardin Shan'xi na arewa maso yammancin kasar Sin wadda aka kira ta da cewar wai "tsohon sauti", da Sinanci ake cewa "Laoqiang". Wurin Bailuyuan yana dab da birnin Xi'an, hedkwatar lardin Shan'xi na kasar Sin. Wurin yana kasancewa a makekiyyar shiyya. Abubuwan da aka rera cikin wakar suna shafar zaman rayuwa na mutanen wurin. Mr Chen Zhongshi yana kaunar irin al'adun gargajiya mai nuna bajinta da kokarin namiji da aka yi ba tare da shiryawa sosai ba. Ya ce, shi kansa manomi ne, ya sha more irin al'adu tun daga karaminsa har zuwa girmansa , yana kan ganin himmar da manoma suke nunawa wajen zaman rayuwarsu na fama da wahalhalu masu yawan gaske, shi ya sa yana kan mayar da irin zaman rayuwar manoma don ya zama babban batun da ke cikin littafinsa. Hanyar da ya bi daga wani manomi zuwa mashahurin mawallafi ita ma tana kunshe da yadda aka fama da yamutsatsen hali tare da wahalhalu masu tsanani.

A shekarar 1942, An haifi Mr Chen Zhongshi a wani kauyen da ke shiyyar Bailuyuan, dukkan iyayensu manoma ne. Da ya ke shi da wansa ba su iya samun damar karatu a sa'I daya ba bisa sanadiyar fama da talauci a tsakanin mutanen iyalinsu, shi ya sa a lokacin da Mr Chen Zhongshi ya cika shekaru 19 da haihuwa, sai ya ga tilas ne ya koma gida daga makarantar sakandare. Amma mafarkin Mr Chen Zhongshi na yin karatu a jami'a bai cika ba .

Bayan da ya koma gida daga makarantar sakandare, ya taba aikin koyarwa a kauye cikin shekaru 6. Da rana, ya yi kokarin aiki domin yara, in dare ya zo, sai ya sami damar wallafa littafi. Sa'anan kuma ya sami aiki cikin shekaru goma a gwamnatin wani garin kauye bisa sakamakon da ya samu wajen aiki.

A wannan lokaci, ya yi cudanya da manoma kai tsaye, ya san kome da kome dangane da zaman rayuwar manoma da kauyuka. Shi ma ya shiga aikin noma , ya ce, a cikin kagaggen labarin da ya wallafa, ba sau daya ba sau biyu ba ya bayyana yadda manoma suke aikin noma, ya bayyana cewa, dole ne ana yin fasahar yada alkama a sama yadda ya kamata don fitar da wasu abubuwan da ba su da amfani, idan iska ba ta da karfi, to ba za a iya fitar da abubuwan da ba su da amfani ba.

Ya ce, a cikin shekaru fiye da goma da suka wuce, ya fahimci manoma sosai da sosai, wannan ne daraja sosai gare shi wajen wallafa littafi. Littattafan da ya wallafa na da yawa.

Kodayake Mr Chen Zhongshi ya taba samun damar yin zaman rayuwa a birni don yin aikin musamman na wallafa littattafai , amma ya ki, ya ci gaba da zamansa a kauyen da aka haife shi. ya bayyana cewa, da na koma kauyen da aka haife ni, gidana ya riga ya lalace, amma na yi kudurin ci gaba da zaman rayuwata a ciki. Tebur da ke cikin gidana tsoho ne da kakana ya bari kuma aka daure shi da igiyoyi, sai na cire tsofaffin igiyoyi , na sake daure tebur din da sabbin igiyoyi don inganta shi. Alamar da ta bayyana kyautatuwar zaman rayuwata ita ce, na iya yin amfani da kwal don dumama dakina.

Bayan shekaru 4 da suka wuce, Mr Chen Zhongshi ya kammala rubuta wani littafi mai suna Bailuyuan, littafin ya sami suna sosai a kasar Sin, a shekarar 1998, littafin nan ya sami lambar yabo na Mao Dun. Mr Mao Dun shi ne mashahurin mawallafin kasar Sin, mutanen kasar Sin sun nuna girmamawa sosai gare shi, yanzu ya riga ya mutu, amma littattafai da ya rubuta sun yi suna sosai a gida da kasashen duniya.(Halima)