Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-16 21:33:08    
Birnin Beijing zai samar da hidima sosai ga aikin jiyya a gun taron wasannin Olympic.

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, wakilinmu ya bakunci Madam Deng Xiaohong, mataimakiyar hukumar kiwon lafiya ta birnin Beijing, inda ta fayyace, cewa an shiga muhimmin mataki kan aikin bada tabbaci ga samun jiyya sosai a duk tsawon lokacin taron wasannin Olympic na Beijing, wato ke nan yanzu ana gudanar da ayyuka kamar yadda ya kamata na game da za a bada aikin jiyya ga 'yan wasa da jami'ai na kasashe daban-daban da kuma shawo kan matsalolin ba-zata na lafiyar jama'a. Madam Deng Xiaohong ta fadi, cewa gwamnatin birnin Beijing za ta samar da aikin hidima mai kyau ga taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Jama'a masu saurare, muhimman ayyuka guda biyu ne za a yi game da yunkurin bada tabbaci ga yin jiyya domin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Muhimmin aiki na farko, shi ne bada tabbaci wajen yin jiyya ga 'yan wasa da jami'ai na gida da na waje, wadanda suke da nasaba sosai da gasanni ; Wani muhimmin aiki daban, shi ne kafa tsarin bada tabbaci ga shawo kan matsalolin ba-zata na lafiyar jama'a a fadin duk birnin Beijing. Madam Deng Xiaohong ta yi farin ciki da fadin cewa dukan ayyukan na gudana lami-lafiya. Sa'annan ta ce : ' Yanzu a nan birnin Beijing, akwai filaye da dakunan gasanni guda 36, da filaye da dakunan horaswa guda 41 da kuma filaye da dakunan da ba na gasanni ba guda 7. Aikin da muke yi yanzu, shi ne tsara shirye-shiryen ayyuka na samar da kyakkyawan ingancin aikin hidima na yin jiyya ga kauyen dukan 'yan wasa da kuma filaye da dakunan wasannin motsa jiki, da tabbatar da zababbun asibitoci guda 20 domin taron wasannin Olympic, wadanda za su bada aikin hidima ga wadannan filaye da dakunan wasannin motsa jiki.

Madam Deng Xiaohong ta kuma ce, bisa bukatar taron wasannin motsa jiki na nakasassu, gwamnatin birnin Beijing ita kuma za ta kafa na'urori marasa shinge a wasu zababbun asibitoci ; Ban da wannan kuma, yanzu ana gudanar da aikin horar da masu aikin jiyya da abun ya shafa da kuma tabbatar da lambobin harsunan waje da dai sauransu.

Game da aikin shawo kan matsalolin ba-zata na lafiyar jama'a, gwamnatin birnin Beijing tana nan tana kafa wani cikakken tsarin giza-gizan sadarwa na internet na yin ceto cikin gaggawa a duk farin birnin. Yanzu, an rigaya an kafa wani tsarin yanke shawara kan tinkarar matsalolin ba-zata na lafiyar jama'a da kuma wani dandamalin ba da jagoranci. Ban da wannan kuma, manyan hukumomin jiyya sama da 700 na duk birnin sun tabbatar da burin gabatar da rahotanni kai tsaye ta internet game da yanayin annobar cututtuka masu yaduwa. Kazalika, gwamnatin birnin Beijing ta kafa wasu hukumomin aiki na musamman masu sa ido kan munanan cututtuka masu yaduwa da kuma giza-gizan sadarwa na internet na yin ceto cikin gaggawa a wasu ni'imtattun wuraren yawon shakatawa. Dadin dadawa, gwamnatin birnin ta tsara jerin shirye-shiryen tinkarar matsalolin ba-zata na lafiyar jama'a.

Madam Deng Xiaohong ta dauki matsalar harin ta'addanci ta halittu masu rai kamar misali : a 'yan shekarun baya, an taba samun matsalolin harin ta'addanci a kasashen waje a fannin ciwon Anthrax, da ciwon cholera da kuma harhada magunguna har da barazanar makaman nukiliya da kuma jerin fashewar boma-bomai da dai sauransu. Sakamakon haka, aka fito da wasu shirye-shiryen tinkarar wadannan matsalolin ba-zata. A nata bangaren, gwamnatin birnin Beijing ta tsara shirye-shiryen shawo kan wasu matsalolin ba-zata kamar na annobar cutar SARS da ta auku a 'yan shekarun baya a nan birnin Beijing. Madam Deng ta ce, a wannan shekara, za a yi gwaje-gwajen aiki da wadannan shirye-shirye, ta yadda dukkan ma'aikatan da abun ya shafa za su iya sauke nauyin dake bisa wuyansu na shawo kan matsalolin ba-zata.

A karshe dai, Madam Deng Xiaohong ta furta, cewa makasudin aikin bada tabbaci ga yin jiyya a lokacin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, shi ne a duk tsawon lokacin taron wasannin, yin watsi da yiwuwar gamuwa da barkewar munanan cututtuka masu yaduwa a yankin Beijing, da shawo kan sabbin ciwace-ciwace masu yaduwa daga ketare, da magance muhimman matsalolin cin abinci mai guba ; Ban da wannan kuma, za a iya magance matsalolin cin abinci mai guba da kuma na shan kazamcewar ruwa a kauyen 'yan wasa, da filaye da dakunan wasanni, da kuma otel-otel da dakunan cin abinci dake shafar taron wasannin Olympic, da kawar da matsalolin ba-zata na lafiyar jama'a cikin lokaci da kuma bada tabbaci ga yin jiyya da kyau ga kowane mutum mai jin rauni da kowane mai rashin lafiya a duk lokacin a ake gudanar da gasannin Olympic. (Sani Wang )