Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-16 21:27:48    
Kasashen duniya sun ci gaba da mai da hankali kan taruruka biyu na kasar Sin

cri
A cikin 'yan kwanakin nan, kasashen duniya da kafofin yada labaru na ketare da sanannun mutane sun cigaba da mai da hankulansu kan rahoto kan aikin gwamnati da firayin minista Wen Jiabao ya yi da daftarin dokar ikon mallakar dukiyoyi da daftarin dokar haraji kan kudin shiga na masana'antu da aka zartas a gun babban taron majalisar dokokin kasar Sin.

Wani jami'in ma'aikatar tattalin arzikin kasar Holland ya ce yana yaba wa daftarin wadannan dokar haraji kan kudin shiga na masana'antu. Yana ganin cewa, wannan doka za ta sanya a yi takara a kasuwannin kasar Sin cikin adalci, kuma za ta yi amfani ga masana'antu kan yadda za su kyautata karfin yin takara a kasuwannin kasa da kasa.

A cikin wani bayanin da aka buga a kan shafin mujallar "Economist" ta kasar Ingila da aka wallafa ta kwanan nan, an ce, tsara dokar ikon mallakar dukiyoyi da kasar Sin ta yi, alama ce ga nasarorin da kasar Sin ta samu domin ta yi gyare-gyare kan tattalin arzikinta da daidaita al'amura iri iri bisa doka. Wannan yana kuma bayyana cewa, yanzu kasar Sin ta fi mai da hankali kan zaman rayuwar jama'a da ra'ayoyinsu. (Sanusi Chen)