Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-16 21:24:17    
Kasar Sin na fitar da kayayyakin al'adu zuwa kasashen waje

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin tana bunkasa harkokin al'adu cikin kwazo da himma, kayayyakin al'adu da yawa wadanda ke da sigogin musamman na kasar Sin suna samun karbuwa sosai daga wajen jama'arta, sa'an nan kuma wasunsu da aka fitar zuwa kasashen waje su ma suna samun karbuwa a kasuwanni. A sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da ingantuwar hadin kanta da kasashen duniya, mutanen kasashen waje za su kara samun damar more idonsu da silima da littattafai da wasannin fasaha na kasar Sin.

A karshen shekarar bara, a karo na farko ne aka shirya bikin baje koli na kasa da kasa na kayayyakin kirkire-kirkiren al'adu a birnin Beijing. Kungiyoyin al'adu da yawa sun nuna kayayyakinsu masu sigogin musamman ga maziyartan gida da na waje. A gun bikin, kungiyar nuna wasannin fasaha ta lardin Jilin da ke a rewa maso gabashin kasar Sin ta buga kida da wani irin kayan kida na gargajiyar kasar Sin da ake kira "Guzheng" cikin Sinanci. Maziyartan sun yi sha'awar kayan kidan nan kwarai da gaske. Malam Wang Guangming, babban manajan kamfanin al'adun kayan kidan "Zheng" na kasar Sin ya bayyana cewa, "kayan kida mai suna "Guzheng" babban kayan kida na gargajiyar kasar Sin ne da muka nuna a gun bikin nan. Yanzu, kasashen Amurka da Jamus da sauransu sun riga sun daddale yarjejeniyar farko a tsakaninsu da kamfaninmu game da nuna wasannin fasaha, don gayyatar mu don gabatar da wasanni da koyar da su a wadannan kasashe."

A gun bikin baje kolin da aka shirya a wannan gami a birnin Beijing, an kuma nuna kayayyakin al'adu masu sigogin musamman iri-iri da yawa, wadanda suka nuna babban ci gaba da aka samu wajen yin harkokin al'adu a kasar Sin. Bikin kuma ya zama wata sabuwar hanya ce da ake bi wajen fitar da kayayyakin al'adu na kasar Sin zuwa kasashen waje.

Yanzu, kayayyakin al'adu na kasar Sin sun fara samun karbuwa daga wajen gamayyar kasa da kasa a hankali a hankali. Malam Li Huailiang, shugaban cibiyar nazarin harkokin cinikayyar al'adu na waje ta Jami'ar Koyon Aikin Watsa Labaru ta Beijing ya jiku sosai da cewa, "a gun bikin baje-koli na littattafan duniya da aka shirya a karo na 58 a birnin Frankfurt na kasar Jamus a shekarar bara, a karo na farko ne, kasar Sin ta sami rarar kudi wajen yin cinikayyar littattafai da ikon mallakar ilmin fasaha. Mun sayar da ikon mallakar ilmin littattafai da yawansu ya wuce 6,000. Wannan wani al'amari ne mai muhimmanci gare mu, kuma ya faranta ranmu kwarai."

Ko da yake a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kayayyakin al'adu na kasar Sin sun fara tsayawa kan matsayi mai rinjaye a kasuwannin kasa da kasa, amma duk da haka ba su da karfi sosai wajen yin takara ba. Malam Li Huailiang yana ganin cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin kasar Sin ta makara ta fara aiwatar da harkokin al'adu ta hanyar kasuwanni. Ya nuna cewa, bisa ci gaba da ake samu wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin, nagartattun al'adun kasar Sin wadanda ke da dogon tarihi na shekaru dubai zai kara samun karbuwa daga wajen baki 'yan kasashen ketare. Ya ce, "a fannin harshenmu, yanzu, mutane da yawa na kasashen waje suna sha'awar koyon Sinanci, kuma an kafa kolejojin Confucius da yawa a kasashen waje. Bisa ci gaba da masana'antun kasar Sin ke samu wajen kara jawo kasuwannin duniya, su ma za su kara samun bunkasuwa cikin sauri, daidai kamar yadda kasar Sin ta sami ci gaba wajen bunkawa harkokin tattalin arzikinta." (Halilu)