Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-16 18:55:45    
Kasar Sin na samun ci gaba ta hanyar adalci da dimokuradiyya

cri

Ran 16 da ran 15 ga wata, an rufe taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin wato NPC da kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wato CPPCC. Wadannan manyan taruruka 2 da aka saba shiryawa a ko wace shekara dandali ne na nuna dimokuradiyya ta sigar musamman ta kasar Sin, haka kuma sun kasance tamkar taga ce mafi kyau da ke bayyana zaman al'ummar siyasa na kasar Sin da kuma manufofinta na bunkasuwa. Raya zaman al'ummar kasar Sin ta hanyar adalci da dimokuradiyya labari ne da ya fi jawo hankula da aka samu daga wadannan taruruka 2 a wannan shekara.

Firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ya mayar da daidaita batutuwan zaman rayuwar jama'a da suka kawo illa ga shimfida adalci a zaman al'umma a matsayin muhimman abubuwa da ke cikin rahoto kan ayyukan gwamnatin Sin a wannan shekara. Matakai a jere kan batutuwan zaman rayuwar jama'a da aka tanada cikin rahoton sun bayyana niyyar gwamnatin Sin a fannin yin amfani da kudade don kiyaye adalci a zaman al'umma. A lokacin taron, maganganu a jere da suka shafi shimfida adalci a zaman al'ummar kasar, kamar su raya kauyuka da aikin ba da ilmi da hauhawar farashin gidaje da yin gyare-gyare kan tsarin ba da magani da dai sauransu sun sha jawo hankulan wakilan jama'ar kasar da kuma 'yan majalisar CPPCC.

Kasar Sin ta samar da abin al'ajabi, wato samun saurin bunkasuwa har na tsawon shekaru misalin 30, ta kuma kyautata zaman rayuwar jama'arta sosai, sa'an nan kuma, ta tabbatar da raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi a duk kasar bayan da ta warware matsalar rashin abinci da tufafi. Sakamakon da Sin ta samu daga wajen ci gabanta ya kyautata zaman rayuwar dukan jama'ar Sin da kuma kara kudaden shigarsu, amma a sa'i daya kuma, ta gamu da wasu matsaloli. Yana kasancewa da gibi a tsakanin birane da kauyuka da wurare daban daban, gibin da ke tsakanin masu fama da talauci da masu kudi yana ta karuwa, aikin ba da ilmi a kauyuka na baya-baya, ban da wannan kuma, tsarin ba da tabbacin zaman al'umma bai sami kyautatuwa ba. An sami wadannan matsaloli da suka shafi adalcin zaman al'ummar kasa a lokacin da ake raya kasar Sin, amma idan an dade ba a warware su ba, to, za su kawo illa ga samun bunkasuwar dukkan kasar Sin mai dorewa yadda ya kamata.

Muhimman dokoki 2 wato 'dokar ikon mallakar dukiyoyi' da 'dokar haraji kan kudin shiga na masana'antu' da aka zartas da su a gun taron shekara-shekara na majalisar NPC a wannan shekara sun biya bukatar da ake ta yi don neman adalci a zaman al'ummar Sin a shekarun baya da suka wuce.

Hakazalika kuma, dimokuradiyya ita ma ta jawo hankali sosai a gun muhimman taruruka 2 a wanann karo. An tsawaita lokacin taro kadan a shekarar bana, in an kwatanta da na shekarun baya da suka shige, ta haka, wakilan jama'ar kasar da 'yan majalisar CPPCC sun iya samun isasshen lokaci don yin tattaunawa da ba da shawarwarinsu sosai kan shirin doka ta 'dokar ikon mallakar dukiyoyi' da ta 'doka kan haraji kan kudin shiga na masana'antu'.

A gun taron shekara-shekara na majalisar NPC da kuma majalisar CPPCC da aka shirya a shekarar da muke ciki, wakilan jama'ar kasar da 'yan majalisar CPPCC sun bayyana ra'ayoyinsu daban daban kan batutuwa da yawa, sun gabatar da shirye-shirye daban daban, wadanda suka shafi kara kudin shiga na manoma da yaki da babakere da sa kaimi kan shimfida dimokuradiyya tun daga tushe da kuma ayyukan shirya taron wasannin Olympic na Beijing da dai makamantansu. Fasahar yada labaru ta zamani na kyautata hanyoyin shiga cikin harkokin dimokuradiyya, wakilan jama'a da 'yan majalisar CPPCC sun dauka ra'ayoyin jama'a ta hanyar Internet, kuma masu amfani da Internet sun yi wa firayim ministansu tambayoyi misalin dubu dari 1 da 20.

Bugu da kari kuma, soke-soken da 'yan majalisar CPPCC suka yi wa wasu hukumomin gwamnatin da kananan hukumomi saboda ba su yi ayyukansu yadda ya kamata ba sun tilasta wa manyan jami'ai da dama su roki gafara daga jama'a. Hakan ya nuna cewa, manyan taruruka 2 na ta samun kyautatuwa, sun sa kaimi kan ci gaban dimokuradiyya ta sigar musamman ta kasar Sin yadda ya kamata.(Tasallah)