Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-16 17:25:35    
Firayin ministan kasar Sin ya amsa tambayoyi game da zaman rayuwar jama'a da yaki da cin hanci da rashawa

cri

A gun taron manema labaru da aka shirya bayan rufe taron shekara shekara na majalisar wakilai ta jama'ar kasar Sin a ranar 16 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya amsa tambayoyin da manema labaru na gida da na ketare suka yi masa game da zaman rayuwar jama'a da yaki da cin hanci da rashawa da dai sauransu.

Da aka tabo magana a kan zaman rayuwar jama'ar kasar Sin, Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kyautata zaman rayuwar mutane da kungiyoyi masu masu fama da talauci ta hanyar kyautata tsarin shari'a na kasar Sin. Mr Wen Jiabao ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta riga ta soke kudin haraji na aikin noma da kudin haraji na kayayyakin musamman na gona, kuma kasar Sin ta gudanar da tsarin ba da ilmin tilas na shekaru 9 ba tare da biyan kudi, kuma ta kafa doka a kan wannan batu. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta aiwatar da tsarin tabbatar da mafi karancin jin dadin rayuwar jama'a, ban da wannan kuma, kasar Sin tana shirin yin gyare gyare a kan aikin kiwon lafiya na garuruwa da kauyuka. Lallai dukkan wadannan matakai da kasar Sin ta dauka za su ba da taimako ga aikin inganta zaman rayuwar mutane da kungiyoyi masu fama da talauci.

Game da aikin yaki da cin hanci da rashawa, firayin minista Wen Jiabao ya fadi cewa, za a kawar da halin tattara iko ba kamar yadda ya kamata ba, kuma za a kara sa ido a kan gwamnatin kasar Sin. Mr Wen Jiabao ya kuma jaddada cewa, game da matsalar cin hanci da rashawa, duk ko wane fanni, duk ko wane mutum, kome muhimmin mukamin da ya kama, za a yanke masa hukunci mai tsanani bisa doka.(Danladi)