Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-15 17:50:34    
Ya kamata al'adu ya taka muhimmiyar rawa wajen yin cudanya tsakanin Sin da kasashen waje

cri

Batun yadda za a iya kara yin musayar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen waje yana daya daga cikin batutuwan da suke jawo hankulan 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin sosai. Wasu 'yan majalisar sun gaya wa wakilinmu cewa, kara yin mu'ammala da hadin guiwar al'adu tsakanin kasar Sin da kasashen waje yana da amfani kwarai ga yunkurin kara fahimtar juna da aminci a tsakanin jama'ar Sin da na kasashe daban-daban, kuma yana da muhimmiyar gudummawa ga cigaban huldar da ke tsakanin Sin da sauran kasashen duniya.

Bikin nuna zane-zanen kasar Amurka da aka shafe shekaru dari 3 da suka wuce da ake yi a nan birnin Beijing yana daya daga cikin ayyukan yin musayar al'adu tsakanin Sin da Amurka. Wannan ne kuma bikin nuna zane-zanen Amurka mafi girma da aka shirya a nan kasar Sin, kuma yana jawo hankulan jama'ar kasar Sin da yawa. Sun Jie, wata daliba wadda ke kallon bikin ta ce, "Yau na zo nan domin kallon wannan bikin nuna zane-zanen kasar Amurka musamman. A da, an taba shirya bukukuwan nuna al'adun kasashen Rasha da Faransa a cikin wannan dakin nuna zane-zane na kasar Sin. Na taba kallonsu duka. Wasu malamai sun gaya mana cewa, misalin yau da shekaru 20 da suka wuce, tattalin arzikin kasarmu yana matsayin koma baya, kasar Sin ba ta da matsayi a duniya. Sakamakon haka, wasu mutanen waje ba su son shirya irin wadannan bukukuwa a nan kasar Sin. Amma, yanzu muna alfahari sosai domin ana shigar da irin wadannan kyawawan bukukuwan nuna zane-zanen kasashen waje a kasar Sin."

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an riga an shirya irin wadannan bukukuwan nuna zane-zanen kasashen waje a kasar Sin har sau da yawa. Lokacin da yake tabo irin musanye-musanyen al'adu tsakanin Sin da kasashen waje, Mr. Jin Shangyi, dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kuma shugaban kungiyar masu yin zane-zane ta kasar Sin yana ganin cewa, wannan kyakkyawan sakamako ne na cigaban tattalin arziki da al'adu tare. "Da farko tattalin arziki, tushe ne ga musayar al'adu. Yau da shekaru 10 ko 20 da suka wuce, mun fara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare kan tattalin arzikin kasarmu. Muna kuma bukatar yin musayar al'adu, amma babu da kudi. Sakamakon haka, ayyukan yin musayar al'adu a tsakaninmu da kasashen waje sun yi kadan. Amma, yanzu, tattalin arzikinmu yana ta samun cigaba, musamman a cikin shekaru 2 da suka wuce, yawan ayyukan yin musayar al'adu tsakaninmu da kasashen waje yana ta karuwa."

Sannan kuma, Mr. Wang Meng, wani mashahurin marubuci ne kuma dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya ce, ya zuwa yanzu, yawan kwalejojin Confucius da aka kafa a yankunan daban-daban a duk fadin duniya ya riga ya kai fiye da dari 1. Wannan kuma hanya ce mai kyau ga kasashen waje wajen sanin kasar Sin. "Muna da kwalejojin Confucius da yawa a duk duniya. Ana yin bukukuwan nuna al'adu da wasannin kwaikwayo da sinima da shirye-shiryen talibijin yayin da ake kuma koyar da harshen Sinanci da fasahohin girkin miyan Sinawa da Chinese Kongfu da zane-zanen gargajiya na kasar Sin. Yanzu ana mai da hankali sosai wajen yin musayar al'adu a tsakanin kasa da kasa. Kasar Sin kasa ce wadda ke da wadatattun albarkatun al'adu."

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin tana kara karfin kiyaye kayayyaki da abubuwan tarihi irin na al'adu. Yanzu, kwararru na dakin ajiye kayayyakin tarihi na kasar Sin suna binciken kayayyakin tarihi a yankin tekun da ke kewayen tsibirin Paartti na kasar Kenya. Wannan ne karo na farko da kasar Sin da kasashen Afirka suka hada guiwa wajen binciken kayayyakin tarihi. Mr. Shan Qixiang, shugaban hukumar kula da harkokin kayayyakin tarihi ta kasar Sin kuma dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar ya bayyana cewa, "Dalilin da ya sa muka yi hadin guiwa tare da kasar Kenya wajen binciken kayayyakin tarihi shi ne muna son gano tarihin dangantakar sada zumunta tsakanin kasar Sin da kasashen gabashin Afirka, musamman tsakanin kasar Sin da kasar Kenya. Yanzu, yawan yin irin wannan hadin guiwa yana ta karuwa." (Sanusi Chen)