Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-15 17:47:42    
Kan yadda aka samu shawarar da 'yan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na kasar Sin (Babi na daya)

cri

A ran 29 ga Janairu na shekara ta 2007,kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da Majalisar Gudanarwa sun bayar da wata takarda wadda ta tanadi wasu shawarwarinsu kan kara bunkasa aikin gona na zamani da gina sabbin kauyuka iri na gurguzu,a cikin babi na uku na sashe na biyu da ke cikin takardar,an tanadi cewa "kamata ya yi a gaggauta bunkasa makamashi mai tsabta a cikin kauyuka".Wannan kalma ta samo asali ne daga cikin wata shawarar da wani dan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mr Liu Chenguo ya bayar.

A gun zama na biyar na majalisar ba da shawarwar da ake yi a nan birnin Beijing,wakiliyar gidan rediyonmu ta yi hira da Mr Liu wanda ya ke halartar zaman,ya gaya wa wakiliyarmu cewa a zaman majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa da aka yi a shekarar bara,babban sakatare na jam'iyyar kwaminis ta Sin Hu Jintao ya mika gaisuwarsa ga 'yan majalisar mahalartan zaman,ya yi fatan 'yan majalisar da su yi nazari da ba da shawarwari kan gina sabbin kauyuka na zamani.Bisa nakalin da babban sakatare Hu Jintao ya bayar,'yan kwamiti na yawan mutane da muhalli na majalisar ba da shawarwari sun yi nazai cikin natsuwa,sun mai da batun samun makmashi mai tsabta a kauyuka muhimmin batu da za sa kai wajen bincike,daga baya 'yan kwamitin sun yi bincike a larduna 12 ciki har da lardunan Hebei da Hunan da Sichuan kan gina sabbin kauyuka na zamani.

Jama'a masu sauraro,ayyukan samar da makamashi mai tsabta a kauyuka sun hada aikin tsabta ce filayen noma da aikin tsabta ce gidajen zama da kuma aikin tsabta ce wuraren ruwa.Ana nufin cewa kamata ya yi a mai da kashin mutum da na dabbobi,da karar shuke-shuke da kuma juji da ruwa mai datti su zama taki da makamashi da kuma abincin dabbobi,ta haka kuwa ake samun sakamako mai kyau wajen tattalin arziki da muhalli da kuma zamantakewa.

Bayan da 'yan majalisar suka yi bincike da gwaji a cikin kauyuka 12,sun bayar da wata shawarar "gaggauta bunkasa ayyukan samun makamashi mai tsabta a kauyuka".Kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin ya dora muhimmanci kan shawarar nan.Mr Liu Chenguo ya ce"A lokacin da muke yin bincike,mumn samu cigaba kuma mun tattara fasahohi a kauyukan dake yin gwaji,duk da haka muhimmin abun dake gabanmu shi karancin kudi.batun samun makamashi mai tsabta a kauyuka,batu ne da ya kamata gwamnati ta kashe kudi a kai.bayan da suka yi nazari,sun bayar da shawarar gaggauta ayyukan nan,kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ya dora muhimmanci kan batun nan.Mataimakan firayim ministaa Zeng Peiyan da Hui Liangyu sun bayar da muhimmin nakali,daga baya aka rubuta wannan shawara cikin takarta mai lamba daya ta kwamitin tsakiya a shekara ta 2007.

Yayin da aka nemi ra'ayinsa kan shawarar da aka rubuta cikin takardar kwamitin tsakiya ta lambanwan,Mr Liu Chenguo dan majalisar ba da shawarwarin ya ce "Lalle mun yi farin ciki da ganin daukar shawararmu da aka yi,wannan ya ba da shaida cewa kwamitin tsakiya da majalisar gudanarwa sun dora muhimmanci kan batun nan.Wannan nasara ce da muka samu.A kan matsayin 'yan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa.muddin ka sarke nauyinka cikin natsuwa,ka ba da shawarwari masu amfani,wadannan shawarwarin za su iya taka muhimmiyar rawa wajen gaggauta bunkasar Sin.

(Za a cigaba)