Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-15 15:34:06    
Ana yin shawarwari masu kyau a tsakanin bangarori daban- daban da suke shafar matsalar nukiliya ta Korea ta Arewa

cri

Bayan ziyarar da Mr. Mohammed el Baradei, babban jami'in hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya yi a ran 14 ga wata a Korea ta Arewa, ya fayyace cewa, Korea ta arewa ta bayyana cewa tana son sake shiga cikin hukumar makamashin nukiliya ta duniya. A wannan rana kuma, ma'aikatar kudi ta Amurka ta dauki wata dabara mai sassauci, wato ta cire takunkumin kudi da ta garkama wa Korea ta Arewa. Bisa ci gaban da aka samu wajen halin da ake ciki an ce, a lokacin da bangarori daban-daban da suke shafar matsalar nukiliya ta yankin teku na Korea suke kokarin tabbatar da alkawuran da suka dauka a matakin farko, kuma suna yin shawarwari masu kyau a tsakaninsu.

A ran 14 ga wata, Mr. Mohammed el Baradei, babban jami'in hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya karasa ziyarar da ya yi cikin kwanaki 2 a Korea ta Arewa. Lokacin da yake bayyana sakamakon da ya samu a gun ziyarar a wurin taron manema labarun da aka shirya a nan birnin Beijing, ya bayyana cewa, ziyarar da ya yi a Korea ta Arewa tana da amfani sosai, wato ta bude babbar kofa ta mayar da dangantaka tsakanin hukumar makamashin nukiliya ta duniya da Korea ta arewa. Korea ta arewa tana son yin hadin gwiwa sosai a tsakaninta da wannan hukuma, kuma za ta rufe kofar gine-ginen nukiliya da ake yi a birnin Yongbyong. Mr. Baradei ya kuma bayyana cewa, Korea ta Arewa tana son cika alkawuranta daga duk fannoni, amma tana bukatar Amurka da ta cire takunkumin kudin da ta sanya mata a farkon farko.

A wannan rana kuma, ma'aikatar kudi ta Amurka ta sanar da cewa, an gama aikin binciken da aka yi cikin watanni 18 kan asusun ajiyar kudi na Korea ta Arewa cikin bankin Macau's Banco Delta Asia wato SARL, kuma ta sanar da cewa tsarin kudi na Amurku ba zai yi cudanya da wannan bankin da ya karbar kudin Korea ta Arewa ba. Ana ganin cewa, wannan matakin da Amurka ta dauka ya alamanta cewa, Amurka ta cire takunkumin kudin da ta garkama wa Korea ta Arewa. Amma har yanzu Korea ta arewa ba ta mai da martani ga wannan matakin da Amurka ta dauka ba tukuna.

Ra'ayoyin jama'a sun bayyana cewa, dalilin da ya sa Korea ta arewa ta dauki jerin matakai masu kyau wajen huldar jakadanci kafin shawarwari na zagaye na 6 da za a yi a ran 19 ga wannan wata a tsakanin bangarori 6 shi ne, domin kara samun hanya mai kyau wajen yin shawarwari, ban da wannan kuma domin ta gane ma idonta kan niyya da burin da bangarori daban-daban da abin ya shafa

suka bayyana, da matakan da suka dauka domin tabbatar da burinsu. Kuma wadannan matakan da aka dauka suna dacewa da ka'idar "mataki kan mataki" da Korea ta arewa ke tsayawa a kullum, sabo da haka, ta yi kokarin yin shawarwari tsakaninta da bangarorin da abin ya shafa domin tabbatar da alkawuran da aka dauka a lokacin farko.

Amma Kafofin watsa labaru su ma sun sa lura cewa, a gun taron manema labarun da aka yi a nan beijing, Mr. Baradei bai bayyana hakakanin lokacin da za a rufe kofar gine-ginen nukiliya da ke birnin Yongbyong ba, kuma bai ambata hakakanin lokacin da sufetocin hukumar makamashin nukiliya ta duniya za su koma Korea ta Arewa ba. Kuma alkawarin da Korea ta arewa ta dauka kan rufewa da kuma jinginar da gine-ginen nukiliya da ke birnin Yongbyong ya zama mataki na farko ne da ta dauka wajen ayyukanta na kawar da makaman nukiliya, ya kasance da hanyar mai nisa kwarai da za ta bi domin cim ma wannan manufa. Daidai kamar yadda Mr. Baradei ya fada cewa, mai da yankin teku na Korea ya zama yankin da ba makaman nukiliya wani yunkuri ne mai yamutsi, yana bukatar bongarori daban-daban da su su kokari domin sake amince wa junansu da yin shawarwari a tsakaninsu, kuma yana bukatar lokaci mai tsawo sosai. (Umaru)