Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-15 10:52:54    
An rufe taron shekara shekara na CPPCC

cri

A ran 15 ga wata da safe a birnin Beijing, an rufe cikakken zama na biyar na shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Ya zuwa lokacin, an kawo karshen taron shekara shekara na wakilan duk kasa na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wanda aka shafe kwanaki 12 ana yinsa. Kudurin siyasa da aka zartas a gun taron ya ce, za a yadada amfanin majalisar wajen daidaita dangantakar da ke tsakanin bangarori daban daban da ba da shawara, ta yadda za a iya bayar da sabon taimako wajen sa kaimi ga bunkasuwar harkokin tattalin arziki da siyasa da al'adu da zaman takewar al'umma na kasar Sin.

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya shugabanci taron rufewa. Taron ya ce, a cikin wannan sabuwar shekara da muke ciki, majalisarsa za ta ba da shawara domin kasar Sin ta cim ma burin samun saurin bunkasuwa ta hanyar kimiyya da fasaha, za ta kara mai da hankali a kan zaman rayuwar jama'a, domin bayyana ra'ayin jama'a da bukatarsu cikin lokaci, da kuma ba da taimako ga gwamnatin kasar Sin da ta warware matsalolin da suke shafar babbar moriyar jama'a. Majalisar kuma za ta kara hada kan dukkan al'ummar Sin a gida da ketare domin cim ma burin dinkuwar kasar Sin gaba daya da farfado da al'ummar kasar Sin.

Taron kuma ya nuna yabo da yarda da rahoto kan aikin gwamnati da firayin minista Wen Jiabao ya gabatar da kuma rahoto kan aikin kotun koli ta jama'ar kasar sin da na hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin da kuma daftarin dokar mallakar dukiyoyi da na haraji da ake bugawa a kan kudin shiga na masana'antu.(Danladi)