Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-14 19:23:23    
Majalisar CPPCC na taka muhimmiyar rawa wajen harkokin siyasa na kasar Sin

cri

'Tun can da, misalin yau da shekaru fiye da 50 da suka wuce, na ba da shawarar mayar da wannan korama a matsayin kayan gargajiya na kasar Sin, sa'an nan kuma, na gabatar da mayar da ita a matsayin kayan tarihi na duniya yau da shekaru 21 da suka wuce.'

Abun da aka ambata a baya kalaman malam Luo Zhewen ne, shi ne shugaban kungiyar masana masu ilmin tsoffin gine-gine ta hukumar kayayyakin gargajiya ta kasar Sin, yana himmantuwa kan kiyaye kayayyakin gargajiya a duk ransa. Koramar da malam Luo ya ambata a baya ita ce wadda ta hada birnin Beijing da birnin Hangzhou, wata mahadar sufuri da ke kudu maso gabashin kasar Sin. Wannan korama mai tsawon kilomita 1794 ta ratsa kasar Sin daga kudu zuwa arewa, an fara haka ta yau da shekaru misalin dubu 2 da dari 5. Ita korama ce da mutane suka haka ta kafin sauran koramu, kuma tsawonta ya fi saura a duk duniya.

Amma wannan muhimmiyar korama ta dade tana fuskantar mawuyancin hali. Yanzu ana yin amfani da koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou mai tsawon kilomita misalin 1442 kawai, koramar mai tsawon kilomita misalin 877 kawai na iya aiki a duk shekara. Don kare wannan korama yadda ya kamata, malam Luo Zhewen ya fara neman shigar da ita a cikin kayayyakin tarihi na duniya yau da shekaru 21 da suka shige, amma ya gamu da matsaloli masu yawa.

A daidai wannan lokaci ne, aikin nan da yake yi ya jawo hankulan 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar wato CPPCC. A lokacin da ake gudanar da taruruka 2 na majalisar dokokin kasar da majalisar CPPCC a shekarar bara, 'yan majalisar CPPCC 58 sun gama kansu sun gabatar da wata shawara game da neman shigar da koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou cikin kayayyakin tarihi na duniya. Bayan wannan kuma, majalisar CPPCC ta tafiyar da aikin musamman na bincike da kara wa juna ilmi kan kiyaye wannan korama da kuma neman shigar da ita cikin kayayyakin tarihi na duniya. Don haka, an kara gaggauta aikin kiyaye koramar da ta hada Beijing da Hangzhou da kuma shigar da ita cikin kayayyakin tarihi na duniya. Shugaban hukumar kula da kayayyakin gargajiya ta kasar Sin Shan Jixiang ya yi karin bayanin cewa, 'A watan Mayu na shekarar bara, majalisar gudanarwa ta kasarmu ta mayar da koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou a matsayin kayan gargajiya da kasarmu ke dora muhimmanci kan kiyaye shi. A watan Disamba kuma, hukumar kula da kayayyakin gargajiya ta kasar ta tanade ta cikin jerin sunayen kayayyakin gargajiya da kasarmu ta yi shirin gabatar da su don zama kayayyakin tarihi na duniya.

Ban da wannan kuma, Liu Feng, wani dan majalisar CPPCC, ya yi bayani kan sauran ayyukan da majalisar CPPCC ke yi don kare koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou, ya ce, 'Majalisarmu za ta ci gaba da kiyaye wannan korama da kuma neman shigar da ita cikin kayayyakin tarihi na duniya. Da farko, ta ba da shawara ga majalisar gudanarwa ta kasar da ta tsara ka'idoji kan kare wannan korama, ta haka za a kiyaye ta bisa dokoki da ka'idoji ta hanyar kimiyya.'

A gaskiya kuma, neman shigar da koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou cikin kayayyakin tarihi na duniya wani bangare ne kawai na sakamakon da majalisar CPPCC ta samu a shekarar bara. Tun daga shekarar bara, bisa ra'ayin kirkire-kirkire ne majalisar CPPCC ta kyautata ayyukan gabatar da shirye-shirye da rangadin aiki da 'yan majalisar ke yi. A shekarar 2006 da ta gabata, bi da bi ne mataimakan shugabanni 13 na majalisar CPPCC suka jagoranci kungiyoyin rangadin aiki 23 da ke kunshe da 'yan majalisar 673 sun je wurare daban daban na kasar don yin nazari domin wasu muhimman shirye-shirye. Wasu muhimman rahotanni da majalisar CPPCC ta gabatar sun samar da muhimman hakikanan abubuwa da karin shawara ga Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin Sin wajen tsara manufofi.(Tasallah)