Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-14 18:19:54    
Takardun masu sauraronmu

cri

Kwanan baya, mun sami wasiku masu yawa daga wajen masu sauraronmu, inda masu sauraronmu suka bayyana ra'ayoyinsu dangane da shirye-shiryenmu tare kuma da ba mu shawarwari.

Dr.Garba Ibrahim Sheka daga jami'ar Bayero, Kano, Nijeriya, ya aiko mana Email cewa, ina duba website dinku kuma ina sauraron shirye shiryenku, kuma ina gamsuwa sosai. Allah ya kara taimakonku. Amin. Ina ba ku shawara da ku kara tsare-tsare domin jawo hankalin masu sauraro domin a rika sauraronku. Wadannan tsare-tsare sun hada da gyara lokacin gabatar da shirye-shirye da kyautata sautin tasharku. Sa'an nan, malam Mahmud Mohammed, mazaunin Ibadan Street Kaduna, jihar Kaduna, Nijeriya ya ba mu shawarar kara lokacin filin karanta wasiku. To, Dr.Garba Ibrahim Sheka da kuma malam Mahmud Mohammed, mun gode maku da ba mu shawarwarinku, wadanda za su taimaka wajen kyautata shirye-shiryenmu, mun gode, muna fatan za ku ci gaba da ba mu goyon baya.

Sai kuma malam Musa Tijjani daga Kadawa Miltara, Kano Nijeriya ya rubuto mana cewa, a gaskiya muna jin dadin shirye-shiryenku, musamman shirin labaru, kuma ina so ku kara ma shirinku lokaci don jin dadin masu sauraronku, kuma ku sani kuna da masoya masu dimbin yawa a nan Nijeriya, musamman jihar Kano, duk inda ka wuce karfe 7:00, agogon Nijeriya, sai dai ka ji sautin CRI na tashi. To, malam Musa Tijjani, mun gode wannan shawarar da ka ba mu, kuma muna so mu sanar da kai cewa, ban da shiri na tsawon rabin awa da muke gabatar muku daga karfe 7 zuwa 7 da rabi a ko wace rana, muna kuma gabatar muku da shirin na tsawon awa daya, wato daga karfe 5:30 zuwa 6:30 na kowace rana, agogon Nijeriya da Nijer da Kamaru, a kan Khz 9665 da Khz 9620, wanda za mu maimaita daga karfe 6:30 zuwa 7:30 a kan Khz 9460 da Khz9780, tare da fatan shirin ba zai wuce ku ba.

Bayan haka, mun kuma sami wasu sakonni daga masu sauraronmu dangane da gasarmu ta kacici-kacici, wato "garin Panda, lardin Sichuan."

Malam Sanusi Isah Dankaba, mazaunin birnin Keffi, jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, kwanan nan na samu sakonku wanda kuka aiko mani da takardun gasar kacici kacici ta garin panda, ko da yake sau da yawa ina shiga gasar kacici kacici ta gidan rediyon kasar Sin, ban taba samun nasara ba, amma ba zan yi kasa ba a gwiwa, saboda mahakurci mawadaci, wata rana in da rabo sai ka ga na dace. Yanzu nan gaba kadan za ku ga amsar tambayoyina a kan gasar kacici kacici dangane da garin panda. Sa'an nan, a cikin sakon da malam Shuaibu Muhammed Rijiyar mai kabi, daga karamar hukumar Kamba, jihar Kebbi, Nijeriya, ya aiko mana, ya ce, shin yaushe ne za a fara gasar garin Panda, ina sauraron amsa daga gare ku. To, madallah, malam Shuaibu Muhammed Rijiyar mai kabi, hakika mun riga mun fara gasar, kuma kawo yanzu, mun riga mun sami amsoshi da yawa daga masu sauraronmu, sabo da haka, muna kira da kai da sauran masu sauraronmu da ba su da wannan labari da ku yi kokarin shiga gasar, ku aiko mana amsa da wur wuri, kuma kuna iya karanta cikakken bayani dangane da gasar a shafinmu na internet, wato www.cri.cn, in kun bude, za ku iya gani a sama. Bayan haka, mun kuma sami wasika daga wajen shugaba Bello Abubakar Malam Gero na kungiyar masu sauraren rediyon kasar Sin ta jihar Sokoto, inda ya ce, ina mai sanar da ku cewa, mun soma samun sakonku na shiga gasar kacici-kacici ta wannan shekara, kuma mun soma aikowa da namu amsoshi, tare da fatan Allah ya ba mu sa'a, Amin. To, mu ma muna muku fatan alheri na cimma kyakkyawar nasara a gasar.

Bayan haka, mun kuma sami sakonni daga wajen Adamu Jibril Maikankana Inkiya Danjuma Jatau unguwan Nungu, jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya da Umar Ibrahim, mazaunin Tudun wada, jihar Kaduna, da dai sauransu, wadanda suka ba mu goyon baya da kwarin gwiwa, to, mun gode, muna fatan za ku ci gaba da ba mu ra'ayoyinku, tare kuma da fatan Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.(Lubabatu)