Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-14 16:14:56    
Tsarin yin mu'amala a lokaci lokaci a tsakanin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da majalisun dokoki na kasashen waje ya samu bunkasuwa sosai

cri
Ran 13 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Jiang Enzhu, babban kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan kasar Sin ya fayyace cewa, a shekarar da ta wuce, tsarin yin mu'amala a lokaci lokaci a tsakanin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da majalisun dokoki na kasashen waje ya samu bunkasuwa sosai.

Ya bayyana cewa, bisa tushen tsara tsarin yin mu'amala a lokaci lokaci a tsakaninta da majalisun dokoki na kasashen Rasha, da Amurka da kuma sauran kasashe 6, da majalisar dokoki ta Turai a 'yan shekarun da suka wuce, a shekarar 2006, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta kara tsara tsarin yin mu'amala a lokaci lokaci bisa matsayi daban daban tare da majalisun dokoki na kasashe guda 7, wato kasashen Afrika ta kudu, da Korea ta kudu, da India, da Australian, da Masar, da Brazil, da Chile, da kuma majalisar dattijai ta kasar Japan. Yanzu, a hakika dai, an riga an tsara babban tsarin yin mu'amala a lokaci lokaci a tsakanin majalisar wakilan jama'ar Sin, da majalisun dokokin kasashen waje.

Mr. Jiang Enzhu ya bayyana cewa, ba za a dakatar da tsarin nan ba, duk da cewar sake zaben majalisar dokoki, da kuma canza manufofi, ta yadda za a iya ci gaba da yin mua'amala kamar yadda suka yi a da, kuma tsarin nan zai ba da taimako mai yakini wajen bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa kamar yadda ya kamata. (Bilkisu)