Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-14 08:23:22    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (07/03-13/03)

cri

Kwanan baya,mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing Li Binghua ya fayyace cewa,daga ran 20 ga wata,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing zai fara haya masu aikin sa kai `yan asalin kasashen waje wadanda ke iya sinanci a duk fadin duniya.Za a gudanar da wannan aiki ne a ofishin jakadan kasar waje daban daban dake wakilci a nan kasar Sin.Mr.Li Binghua ya ce,muna yin marhabun sosai ga mutane `yan asalin kasashen waje da su shiga jeren masu aikin sa kai,amma dole ne suna iya yin magana da sinanci.

Ran 8 ga wata,a hukunce ne tashar internet ta sayar da tikitin zama na 29 na taron wasannin Olimpic da kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya kafa ta fara aiki,mutanen kasar Sin suna iya yin rajista a kan tashar.Tashar nan ita ce tashar internet daya kadai da gwamnatin kasar Sin ta kafa musamman domin samar da labarai da manufofi game da tikitin taron wasannin Olimpic na Beijing,alal misali labarin gasanni da na farashin tikiti da na dabarar sayen tikiti da na cibiyoyin wasanni da sufuri da na yadda ake kallon gasanni da dai sauransu.Amma yanzu dai ba a fara sayar da tikiti ba tukuna.

Ran 10 ga wata,a gun gasar cin kofin duniya ta wasan skiing a tsakanin duwatsu iri na `free style` ta shekarar 2007 da aka yi a birnin Turin na kasar Italiya,`yar wasa daga kasar Sin Li Nina ta zama zakarar mata ta wasan fasaha a cikin sama,`dan wasa daga kasar Sin Han Xiaopeng shi ma ya zama zakaran maza na wannan wasa,wannan karo na farko ne da `yan wasan maza na kasar Sin suka samun lambawan a gun gasar cin kofin duniya ta wasan skiing a tsakanin duwatsu iri na `free style`.Han Xiaopeng ya taba samun lambar zinariya ta wannan wasa a gun taron wasannin Olimpic na yanayin sanyi na Turin.(Jamila Zhou)