Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-13 18:21:53    
Kasashen duniya suna mai da hankali kan labarin tarurruka biyu da kasar Sin ke yi

cri

A kwanakin baya, kafofin watsa labaru da kwararru da suka yi suna na kasashen duniya sun mai da hankulansu kan labarun da aka watsa daga taron majalisar wakilan jama'a da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin game da ayyukan gina da kuma bunkasa kasar.

Kamfanin dilancin labaru na gabas ta tsakiya na kasar Masar yana mai da hankali kan tarurruka biyu da kasar Sin ke yi tun lokacin da aka fara yinsu, kuma ya bayar da rahoto cewar kasar Sin tana nazarin sabon manyan roka mai iya daukar kayayyaki, da kuma cewa gwamnatin kasar Sin ta kashe kudi da yawa don kare kayayyakin gargajiya na lardin Tibet, har wa da cewar kasar Sin ta sa kaimi ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yin amfani da makamashin nukiliya.

Mr. Stepgen Perry, shugaban kungiyar kamfannoni 48 na kasar Birtaniya ya ce, dokar ikon mallakar dukiyoyi da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yi, wannan abu ne mai kyau.