Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-13 18:19:31    
Mutanen rukunin addinai na kasar Sin sun shiga harkokin siyasa ta kasar cikin himma da kwazo

cri

Ana gudanar da manyan tarurukan siyasa 2 da aka saba shiryawa a ko wace shekara a nan Beijing, wato babban taro na majalisar dokoki ta kasar Sin da kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar. Mutanen rukunin addinai na kasar su ne suna halartar tarurukan 2.

Ba ma kawai suna mai da hankulansu kan harkokin addinai ba, har ma suna mai da hankulansu kan batutuwan zaman rayuwar jama'a da dai sauransu, shawarwarin da suka bayar sun hada da raya sabbin kauyuka, da rage gibin da ke tsakanin masu fama da talauci da masu kudi, da daidaita gurbataccen ruwa da kuma kiyaye muhalli da dai makamantansu.

Yanzu mutane kimanin 170,000 na rukunin addinai na kasar Sin suna halartar majalisun wakilan jama'a da kuma majalisun ba da shawara kan harkokin siyasa na matakai daban daban.

Kamar yadda wata kwarya kwaryar kididdiga da aka yi ta nuna, an ce, yanzu mutanen Sin fiye da miliyan dari 1 suna bin addinan Buddha da Taoism da Kirista da Katolika da kuma Musulunci da dai sauransu.(Tasallah)