Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-13 17:15:53    
Kasar Sin tana aiwatar da ma'aunin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta a birane da kauyuka

cri

Kamfanin dillancin labari na Xinhua ya ruwaito mana labari cewa, kasar Sin tana aiwatar da ma'aunin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta a birane da kauyuka cikin himma da kwazo, don tabbatar da zaman rayuwar fareran hula masu fama da talauci a birane da kauyuka yadda ya kamata.

A gun taron manema labaru da aka yi a ran 13 ga wata domin taro na 5 na majalisar dokoki ta kasar Sin ta 10, mataimakin ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin Li Liguo ya yi karin haske cewa, bisa kimantawar da hukumomin da abin ya shafa suka yi da kuma ra'ayoyin da rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasar suke bayyanawa, an ce, kasar Sin ta riga ta aiwatar da ma'aunin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta ga dukan 'yan biranen da suke bukata.

Ya kara da cewa, har zuwa karshen shekarar bara, kasar Sin ta aiwatar da ma'aunin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta ga 'yan birane fiye da miliyan 220. Gwamnatin tsakiya da kananan hukumomi na matakai daban daban sun zuba kudaden da yawansu ya kai kudin Sin yuan biliyan 22 ko fiye kan wannan aiki.

Ban da wannan kuma, wannan jami'i ya ci gaba da cewa, ana sa ran cewa, kasar Sin za ta aiwatar da ma'aunin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyuka a watanni 6 na farko na wannan shekara.(Tasallah)