Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-13 17:03:59    
Cibiyar wasannin motsa jiki kan ruwa ta kasar Sin da ke birnin Qingdao

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. A cikin shirinmu na yau, kamar yadda muka saba yi, da farko za mu karata muku wasu abubuwa kan cibiyar wasannin motsa jiki kan ruwa ta kasar Sin da ke birnin Qingdao, daga bisani kuma sai wani bayanin musamman, za mu sake karanta muku shirinmu na musamman na gasar ka-ci-ci ka-ci-ci ta 'garin Panda, lardin Sichuan', inda za mu tabo magana kan ' Gidan Panda, wato shiyyar kiyaye halitta ta gandun daji ta Wolong ta lardin Sichuan'.

An gina cibiyar wasannin motsa jiki kan ruwa a matsayin duniya a birnin Qingdao na lardin Shandong. Cibiyar wasannin motsa jiki kan ruwa ta kasar Sin da ke birnin Qingdao zai bai wa birnin Beijing taimako wajen shugabantar gasannin tseren kwale-kwale da na kananan kwale-kwale na taron wasannin Olympic na lokacin zafi na shekara ta 2008. Birnin Qingdao ya sami wannan kyakkyawar dama ce a ran 13 ga watan Yuli na shekara ta 2001. An soma gina wannan cibiya a shekara ta 2002, wadda fadinta ya kai misalin murabba'in mita 420,000, tana kuma kusa da wani wurin shakatawa na wurin, wato rairayin bakin teku na Fushanwan.

Cibiyar nan ta iya daukar nauyin gasanni da ayyukan horo da harkokin ba da nishadi, sa'an nan kuma, ta kan karbi masu yawon shakatawa. An shimfida manyan hanyoyin mota guda 4 a kewayanta, wato a gabas da yamma da kudu da arewa, ta haka an hada wannan cibiya da cibiyar birnin. An shirya wani yankin ciniki a cikin cibiyar wasannin motsa jiki kan ruwa da ke Qingdao. An kiyasta cewa, 'yan wasan da za su shiga taron wasannin Olympic na shekara ta 2008 za su yi takara mai zafi da juna a nan, za su kuma ji dadin ganin ni'imtattun wurare na Qingdao ta fuskar sararin sama da manyan tsaunuka.

An mayar da wannan cibiyar wasannin motsa jiki kan ruwa tamkar wuri ne mai kyau ga kasar Sin a fannin shirya gasannin tseren kwale-kwale da na kananan kwale-kwale. A cikin shekarun baya da suka wuce, birnin Qingdao ya ci nasarar shirya gasannin tseren kwale-kwale da na kananan kwale-kwale na duniya sau da yawa. A gun gasar fid da gwani ta tseren kwale-kwale ta duniya a karo na 39 da aka yi a nan a kwanaki 10 na tsakiyar watan Yuli na shekara ta 2002, 'yan wasa kimanin 400 daga shiyyoyi da kasashe misalin 45 sun yi karawa da juna don zama zakara. Birnin Qingdao yana kyautata kansa don zama birnin da ke dacewa da shirya gasannin kan ruwa a shekara ta 2008 mai zuwa. Zai kara zuba kudi kan manyan ayyukansa kafin shekara ta 2008, kamar su gaggauta gina tashoshin jiragen ruwa da kuma fadada babban filin jirgin sama nasa.