Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani kan cewa, shan abin sha kadan da ke kunshe da sukari a lokacin yarantaka zai ba da taimako wajen lafiyar jiki. Daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani game da Margaret Chan, sabuwar babbar daraktar kungiyar WHO. To, yanzu ga bayanin.
A 'yan kwanakin nan da suka gabata, kasar Amurka ta bayar da wani rahoton nazari, cewa idan yaro ya sha abin sha kadan da ke kunshe da sukari a lokacin yarantaka, to bayan da ya yi girma, zai rage hadarin kamuwa da ciwon zuciya da na hauhawar jini da kuma na sukari.
Haka kuma rahoton ya bayyana cewa, a da, manya da tsofaffi su kan kamu da ciwon zuciya da na hauhawar jini da kuma na sukari sakamakon samun kiba fiye da kima. Amma a 'yan shekarun nan da suka gabata, wadannan ciwace-ciwace sun fara kai wa matasa barazana. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ba safai matasa su kan ci abinci ko shan abin sha yadda ya kamata ba. Ban da wannan kuma rahoton ya nuna cewa, idan aka dauki tsaurarran matakai a lokacin yarantaka, to bayan da aka yi girma, yiyuwar kamuwa da ciwace-ciwacen da ke da nasaba da sauye-sauyen halitta zai ragu sosai.
Alison Ventura, manazarci na cibiyar nazarin ciwace-ciwacen da yara su kan kamu da su sakamakon kiba fiye da kima ta jami'ar jihar Pennsylvania ta kasar Amurka da abokan aikinsa sun tattara labarai game da yara mata 154 wadanda shekarunsu ya kai 13 da haihuwa domin yin nazari kan bugun jininsu da kugunsu da yawan kitsen da ke taruwa a jijiyoyinsu da kuma yawan sukarin da ke cikin jininsu. Daga baya kuma an gano cewa, dukkan yara mata da bugun jininsu da kuma yawan kitse da sukari da ke cikin jininsu sun yi yawa, nauyin jikinsu ya fi yawa. Kuma muhimmin dalilin da ya sa suka samu kiba fiye da kima shi ne sabo da sun sha abin sha mafi yawa da ke kunshe da sukari lokacin da shekarunsu ya kai 5 zuwa 9 da haihuwa.
Sabo da haka manazarta sun yi hasashen cewa, yaran da suka fi son cin sukari sun fi saukin kamuwa da ciwon zuciya da na hauhawar jini da na sukari idan an kwatanta su da sauran yara. Ban da wannan kuma Mr. Ventura ya nuna cewa, idan aka fara kula da nauyin jiki da kuma shan abin sha kadan da ke kunshe da sukari a lokacin yarantaka, to bayan da aka yi girma, za a iya rage hadarin kamuwa da ciwace-ciwacen da ke da nasaba da sauye-sauyen halitta.
Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani game da Madam Margaret Chan. A ran 4 ga wata, Madam Margeret Chan da ta fito daga shiyyar musamman ta HongKong ta kasar Sin ta hau kujerar babbar daraktar kungiyar kiwon lafiya ta MDD wato WHO, sabo da haka ita ce Basiniya ta farko da ta zama shugabar hukumar musamman ta MDD. Mene ne dalilin da ya sa kasashe masu dimbin yawa suka nuna mata goyon baya da kuma zabe ta da ta zama babbar daraktar kungiya WHO? Kuma bayan da ta hau kan mukamin babbar daraktar hukumar WHO, mene ne za ta yi don shugabantar wannan muhimmiyar kungiyar? to a cikin shirinmu na yau, za mu gaya muku.
|