Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-13 11:05:47    
Majalisar hakkin dan adam ta MDD ta kira taron farko na shekarar da muke ciki

cri

A ranar 12 ga wannan wata a fadar kasashen duniya ta birnin Geneva, babbar hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke Turai , majalisar hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ta kira taron farko na shekarar da muke ciki.

Taron nan da za a yi makonni uku ana yin sa zai dudduba rahotanni fiye da goma wadanda hukumomin da ke karkashin shugabancin tsohon kwamitin hakkin dan Adam suka gabatar, da kuma dudduba rahoton da kungiyar aiki ta yin nazari kan tsarin duddubawa a lokaci lokaci, har da yin nazari kan halin da ake ciki na aiwatar da kuduran da aka tsai da a gun tarurukan musamman guda hudu na majalisar hakkin dan Adam. Sa'anan kuma, zai ci gaba da tattaunawa kan ka'idojin aiki daban daban na Majalisar hakkin dan Adam da kuma shirya taron musamman na yin tattaunawa kan yadda za a daidaita batun nuna karfin tuwo ga yara da kiyaye hakkin nakasassu.

Majalisar hakkin dan Adam da ta soma aiki daga watan Yuni na shekarar da ta shige sakamako ne mai muhimmanci da Majalisar dinkin duniya ta samu wajen yin gyare-gyare. Dayake tsohuwar majalisar hakkin dan Adam ta riga ta zama kayan siyasa na kai wa kasashe masu tasowa lambar matsi da dakalin yin adawa da juna a tsakanin kudu da arewa wajen harkokin siyasa, saboda ta riga ta rasa amincewar da aka yi mata, shi ya sa a shekarar da ta shige, an yi shelar watsi da ita. In an kwatanta ta da kwamitin hakkin dan Adam da ke kasancewa cikin shekaru 60, babban ci gaban da sabuwar Majalisar ta samu ya bayyana a fannoni biyu, wato na farko, ana kula da batun hakkin dan Adam a ko'ina da kuma tabbatar da tsarin yin duddubawa a lokaci lokaci a ko'ina, kuma kasashe daban daban na duniya suna zaman daidai wa daida, za a yi musu duddubawa dukka, an yi watsi da abun da aka yi na yin zabe da aiwatar da ma'auni iri biyu. Na biyu, ana aiwatar da ayyukan a yau da kullum. Za a tsawaita lokacin taron na makkoni 6 a kowace shekara zuwa sau uku a kowace shekara, kuma yawan adadin lokacin taro a kalla zai kai makonni 10 , sa'anan kuma za a iya kira taron musamman na wucin gadi, a sa'I daya kuma, majalisar ta kara yawan mambobin kasashen masu tasowa da kuma watsi da tsarin da aka yi na kasancewar cancantar mambobi a ko da yaushe, yawan lokacin aiki zai kai shekaru 6 ne kawai a sau biyu a jere..

A shekarar da ta shige, majalisar hakkin dan Adam ta kira taruruka sau uku, wato a watan Yuni da watan Satumba da Watan Nuwamba, kuma ya zartas da wasu kudduran kiyaye hakkin dan Adam, kuma ta shirya taron musamman na wucin gadi domin daidaita rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Palesdinu. Amma, bisa matsayin sabuwar hukuma, a dukkan fannoni, har wa yau dai majalisar tana kasancewa cikin lokacin wucin gadi da na tsara sabbin ka'idoji, ba ta kama hanyar aiwatar da ayyuka yadda ya kamata ba.

A gun bikin bude taron, shugaban majalisar hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya , kuma wakilin kasar Mexico da ke wakilci a Majalisar Dinkin duniya da ke Geneva Mr Luis Alfonso De Alba ya karfafa magana cewa, ya kamata majalisar hakkin dan Adam ta kara inganta hadin guiwa da gaske da kuma gyara wasu abubuwan da tsohon kwamitin hakkin dan Adam ya yi da kuma kafa tsarin adalci da na daidaici. Sabon babban sakatare na Majalisar Dinkin duniya Mr Ban Kim-moon ya kuma bayyana cewa, ya yi fatan majalisar hakkin dan Adam za ta yi hadin guiwa bisa daidaici da kuma tsara tsarin duddubawa a lokaci lokaci a ko'ina.

A farkon lokacin kafa Majalisar Hakkin Dan Adam, ta yi shelar ba da taimako ga kasashe daban daban don daidaita batun hakkin dan Adam ta hanyar yin tattaunawa da hadin kai da kuma mai da hankali ga hakkin raya kasa da sauran hakkin dan Adam a manyan fannoni. Amma saboda kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba suna da bambanci a tsakaninsu, shi ya sa ya kasance da sabani mai tsanani a tsakaninsu. (Halima)