Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-12 18:59:24    
Kasar Sin ba za ta canja manufarta ta rage fitar da abubuwan da ke gurbata muhalli ba

cri
A gun taron shekara-shekara da majalisar dokoki ta kasar Sin take shiryawa a nan Beijing, wakilan jama'ar kasar Sin sun mai da hankulansu kan cewa, kasar Sin ba ta tabbatar da makasudin rage fitar da abubuwan da ke gurbata mahalli da ta gabatar a farkon shekarar bara ba, sun ba da shawarwari kan yadda kasar Sin za ta tabbatar da wannan makasudi.

A lokacin da take tsara shirin raya kasa a shekarar bara, kasar Sin ta gabatar da cewa, za ta rage jimlar manyan abubuwan da ke gurbata muhalli da kashi 10 cikin kashi dari a shekarar 2010 bisa ta shekarar 2005, wannan ya nuna cewa, tun daga shekarar bara, dole ne kasar Sin ta rage fitar da manyan abubuwan da ke gurbata muhalli da kashi 2 cikin kashi dari a ko wace shekara. Amma a cikin rahoto kan ayyukan gwamnatin da ya gabatar ga wakilan jama'ar kasar, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ya yi bayanin cewa,'A shekarar 2006 da ta gabata, an rage saurin karuwar jimlar manyan abubuwan da ke gurbata muhalli, amma kasar Sin ba ta tabbatar da makasudin da ta gabatar a farkon shekarar 2006 ba, wato rage fitar da manyan abubuwan da ke gurbata muhalli da kashi 2 cikin kashi dari.'

Wakilan jama'ar kasar Sin sun bayyana ra'ayoyinsu a kan dalilan da suka sa haka.

Malam Wang Mengkui, darektan cibiyar nazarin harkokin bunkasuwa ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin, yana ganin cewa,'Babban dalilin da ya sa haka shi ne domin wasu kananan hukumomi sun nemi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki ne kawai, don haka da kyar za a iya yin watsi da karfin kawo albarka, wanda yake baya-baya ne ainun.'

Malam Zhao Zhiquan da ya zo daga lardin Shandong na gabashin kasar, ya soki hukumomin da abin ya shafa saboda ba su aiwatar da dokoki yadda ya kamata ba.

Madam Zhao Min da ta zo daga lardin Guangdong na kasar ta gabatar da cewa, ba a yanke hukunci sosai kan masana'antun da suka saba dokoki sosai ba.

A cikin irin wannan hali ne, ko za a nace ga tabbatar da makasudin rage fitar da abubuwan da ke gurbata muhalli ko a'a? firayim minista Wen Jiabao ya tsaya tsayin daka kan cewa, kasar Sin za ta nace ga tabbatar da makasudin yin tsimin makamashi da rage bata makamashi da kuma rage fitar da abubuwan da ke gurbata muhalli, ba za ta canza wannan ba.

Saboda haka gwamnatin Sin ta fito da wasu matakai gaba daya, ta bukaci kananan hukumomi da su aiwatar da ma'aunin kiyaye muhalli a tsanake, su yi watsi da karfin kawo albarka, wanda yake baya-baya, su jagoranci masana'antu da su yi amfani da sabbin injuna da fasahohi da ke amfanawa wajen kiyaye muhalli. Sa'an nan kuma za su kara aiwatar da dokoki da sa ido, za su dora laifi kan mutane ko hukumomi ko kungiyoyi da suka yi kuskure.

Game da wannan kuma, wakilan jama'ar kasar sun ba da shawarwarinsu. Malam Mao Rubai da kesa ido kan kwamitin kula da kadarorin muhalli ta majalisar dokokin kasar yana ganin cewa,'Don tabbatar da makasudinta, dole ne kasar Sin ta canja tunanin bunkasuwa, ta dora muhimmanci kan kyautata inganci da riba a fannin raya tattalin arziki, ta mai da hankali kan rage bata makamashi da fitar da abubuwan da ke gurbata muhalli. Sa'an nan kuma, za ta samar da hanyoyin zuba jari, za ta tabbatar da zuba isassun kudade kan rage abubuwan da ke gurbata muhalli. Haka zalika kuma, za ta kara sa ido don tabbatar da aiwatar da dokoki yadda ya kamata. '

Madam Chen Min ta ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatin kasar ta yi gyare-gyare kan dokokin da abin ya shafa don kara yanke hukunci kan masana'antun da suka saba dokoki da ka'idoji.

Ko da yake kasar Sin ba ta cimma makasudinta ba, amma yawancin wakilan jama'ar kasar sun yi imanin cewa, kasar Sin za ta tabbatar da wannan makasudi a sakamakon kokarin da gwamnatin da rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasar suke yi.(Tasallah)