Galibin 'yan kabilar Men Ba na kasar Sin suna zama a shiyyar Menyu da ke kudu maso gabashin jihar Tibet mai cin gashin kanta. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000 a duk fadin kasar Sin, yawan mutanen kabilar Men Ba ya kai kimanin dubu 8 da dari 9 da 23 kawai. Suna amfani da yaren Men Ba, amma babu kalmomi da harufai. Yawancinsu sun iya harshen Tibet.
A da, muhimmiyar sana'ar da 'yan kabilar Men Ba suke yi ita ce, aikin gona tare da ta farauta da tsinci 'ya'yan itatuwa. Sana'ar hannu tana cikin sana'ar aikin gona. Mutane wadanda suke yin sana'ar hannu suna kuma yin aikin gona.
A da al'ummar Men Ba suna zama kamar yadda 'yan kabilar Tibet suke zama suna karkashin mulkin gwamnatin wuri ta Tibet da masu hannu da shuni da masu ikon tafiyar da dakunan abada. Yankunan da 'yan kabilar Men Ba suke zama suna cikin hannun wadannan bangarori 3. Yawancin 'yan kabilar Men Ba su bawa ne.
A shekarar 1951 ce jihar Tibet ta samu 'yanci cikin lumana. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin tsakiya ta kasar sun tura rukunonin aiki zuwa yankunan da 'yan kabilar Men Ba suke zama domin sanin halin fama da talauci da suke ciki. A cikin shekaru fiye da hamsin da suka wuce, tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar Men Ba sun samu cigaba sosai, zaman rayuwar 'yan kabilar ya kuma samu kyautatuwa. Yanzu, 'yan kabilar suna zama a cikin gidajen da ke da wutar lantaki. An kuma shimfida hanyar mota da kafa dakunan jiyya da makarantun firamare a yankunansu.
'Yan kabilar Men Ba sun kware kan yada tatsuniyoyi da baki, musamman sun fi kware kan rerawa wakoki iri iri.. Ana kiran wakokin da suke bayyana zaman rayuwar al'ummar da al'adu da fata da tunani na kabilar wakokin "Sama". A waje daya kuma, ana kiran wakokin soyayya wakokin "Jialu". Sannan kuma akwai wakokin nuna farin ciki. Bugu da kari kuma, sun kware kan nuna wasannin kwaikwayo da suke bayyana zaman rayuwarsu.
Bisa al'adar kabilar Men Ba, wani saurayi yana aurar mace daya. Ba ma kawai suna neman aure a tsakaninsu ba, har ma suna neman aure da 'yan kabilar Tibet da ta Lu Ba da ta Han. Kafin a yi bikin aure, samari da 'yan mata suna da 'yancin zaben abokan soyayya, amma daga karshe dai, suna tabbatar da aurensu ne karkashin taimakawar iyayensu. A cikin gidan 'yan kabilar, maza da mata suna zama cikin halin daidai wa daida, har ma a wasu gidajensu, uwargida tana da ikon tattalin arziki, matsayinta ya fi na mijinta.
Yawancin 'yan kabilar Men Ba suna bin addinin Lama, wani darikar addinin Buddha. Wasu suna bin addinin gargajiya nasu. Ranar farko ta kalandar kabilar Tibet rana ce mafi muhimmanci ga 'yan kabilar Men Ba. Bugu da kari kuma, a watan Yuli, suna taya murnar bikin girbin 'ya'yan itatuwa. (Sanusi Chen)
|