Yanzu mu mai da kwalejin kabilar Yi ta jami'ar a matsayin misali. Furfesa Wuniduoqie, shugaban kwalejin ya gaya mana cewa, lokacin da ake koyar da ilmi, ana jaddada hasashen 'neman ra'ayi daya daga kasancewar bambancin da ake da shi'. Ya zuwa yanzu, kwalejin ta riga ta zama wata muhimmiyar cibiya ta kasar Sin wajen bayar da horo a kan harsunan kabilun Han da Yi duk, da kuma yin nazari kan ilmin kabilar Yi. Ya kara da cewa, "Ko wace kabila tana da al'adunta, amma ana nuna girmama ga al'adu da addinai na dukkan kabilun Sin a jami'ar. Sabo da haka ayyukan nazarin ilmin kananan kabilun kasar Sin sun samu bunkasuwa kwarai da gaske, ban da wannan kuma aikin horar da kwararru 'yan kananan kabilu ya nuna fifiko sosai wanda ba za a iya maye gurbinsa ba."
Dalibai masu yawa da jami'ar kabilu ta kudu maso yammacin kasar Sin ta dauke sun zo daga yankunan da ke da wuyar zuwa da wadanda tattalin arzikinsu suna baya baya. Sabo da haka hukumomin da abin ya shafa na jami'ar suna aiwatar da manufofin da gwamnatin kasar Sin ta tsara cikin yakini wajen samar da kudin taimako, ta yadda za a iya samar da rancen kudin karatu ga dalibai masu fama da talauci. A waje daya kuma, sun yi namijin kokarinsu wajen samar da guraban aikin yi don samun kudin karatu, ta yadda dalibai masu fama da talauci za su iya kammala karatunsu lami lafiya. Luo Wen, wani dan kabilar Zhuang da ke karatu a fannin na'urar kwamfuta yana daya daga cikinsu, kuma ya gaya mana cewa, "Sunana Luo Wen, na zo daga jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Sabo da gidana yana fama da talauci, shi ya sa jami'ar ta samar da damar aiki don samun kudin karatu. Bayan da aka yi mini jarrabawa, na zama mai ba da taimako ga mai kula da samar da rancen kudin karatu na kasarmu domin gudanar da wasu ayyukan jami'armu wajen yin ragista kan neman samun rancen kudin karatu, ta haka na samu taimako kan zaman rayuwata, bugu da kari kuma na koyi abubuwa masu yawa ta yin wannan aiki. "
He Jian, wani saurayi dan kabilar Tibet ne da ya zo daga jihar Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin, yanzu yana karatu a kwalejin harsunan waje ta jami'ar kabilu ta kudu maso yammacin kasar Sin. Kuma ya gaya wa wakilinmu cewa, yana jin dadin zaman jami'ar sosai. ya kara da cewa, "Da na shiga jami'ar, na ji kyakkyawan yanayin al'adu. Kuma bayan da na tuntubi dalibai na kabilu daban daban da na wurare daban daban, na samu karuwa sosai a fannin ilmi da kuma bude ido."
Mr. Zengming, mataimakin shugaban jami'ar kabilu ta kudu maso yammacin kasar Sin ya bayyana cewa, jami'ar ta horar da kwararru masu yawa na kabilu daban daban. Kuma a nan gaba, za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan ra'ayin raya ayyukan koyarwa mai jituwa domin jami'ar ta zama wata jami'ar kabilu ta zamani irin na sabon salo. Kande Gao) 1 2
|