Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-12 16:48:53    
Gaba daya ne kasar Sin ta taimaka wa Afirka bisa sahihiyar zuciya

cri

A ran 12 ga wata a birnin Beijing, ministan kasuwanci na kasar Sin Bo Xilai ya bayyana cewa, gaba daya ne kasar Sin ta taimaka wa kasashen Afirka bisa sahihiyar zuciya.

Mr Bo ya yi wannan bayani ne a gun wani taron manema labaru na babban taron shekara shekara na majalisar wakilai ta jama'ar kasar Sin da aka shirya a ran nan.

Game da ra'ayin da ake dauka wai kasar Sin tana taimaka wa kasashen Afirka ne domin kwashe albarkatunsu, Mr Bo ya ce, cinikin da kasar Sin da kasashen Afirka suke yi a fannin albarkatu ya zama aiki na kasuwa ne bisa farashin adalci. Ban da wannan kuma, a cikin shekaru da dama da suka wuce, kasar Sin ta kafa makarantu 19 da asibitoci 38 ga Afirka, kasar Sin ta ba da taimako ga Afirka wajen gina dakunan wasanni, wadanda yawan kujerun da ke ciki ya kai dubu 760. Lallai kasar Sin tana gudanar da dukkan wadannan ayyuka ne domin taimakawa Afirka a kan sha'anin ilmi da motsa jiki da kiwon lafiya, sabo da haka wadannan ayyuka ba su da nasaba ko kadan da ra'ayi wai kwashe albarkatu da mulkin mallaka. Wadannan ayyuka suna taka wata muhimmiyar rawa wajen kara hadin kai a tsakanin Sin da Afirka.(Danladi)