Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-12 16:33:24    
Sojojin ruwan kasar Sin sun shiga rawar daji da takwarorinsu na kasashen ketare

cri

A cikin shirinmu nau za mu kawo muku wani labari yadda sojojin ruwa na kasar Sin suka samu nasara wajen yin rawar daji da takwarorinsu na sauran kasashen duniya a teku.

Daga ran 8 zuwa ran 11 ga wata a arewancin tekun Larabawa dab da kasar Pakistan,sojojin ruwa na kasashe takwas sun yi rawar daji tare wanda ke da lakabi haka "zaman lafiya?07",sojojin ruwa na rundunar soja ta 'yantar da jama'ar kasar Sin sun shiga wannan rawar daji haka kuma sun sami cikakkiyar nasara kan ayyukan daban daban da suka yi.Wannan shi ne karo na farko da sojojin ruwa na kasar Sin suka shiga rawar daji tare da takwarorinsu na sauran kasashen duniya.

Bayan karar jiniyar fara rawar daji ta fito cikin gaggawa,sai a ran 8 ga wata sai sojojin ruwa na kasashe da dama sun fara rawar daji a teku.Jiragen ruwan yaki guda 12 da suka zo daga kasashen Pakistan da Bangaladesh da Faransa da Italiya da Britaniya da kuma Malasiya da Amurka sun taru sun yi ayyuka 20 na rawar daji da ke da taken yin adawa da ta'addanci.

Wani muhimmin aikin dake gaban sojojin ruwa na kasar Sin shi ne harba takitoci guda biyu,abubuwan leda ne masu launin ruwan lemo da aka kafa kan teku.Jirgin ruwan yaki mai lamba Sanmin da Liangyungang kowanensu ya harba takitocin da ke bisa teku.Da farko jirgin ruwa mai lamba Sanmin ya samu nasarar harbo abin da ya auna.sannan jirgin ruwan yaki mai lamba Liangyungang ya fara aikinsa cikin nitsuwa bisa umurnin kwamandan jerin gwanon jiragen ruwan sojojin Sin babban Kanar Qiu Yanpeng wanda yake bukata a nutsar da abin takitin dake bisa teku. "a juya akalar jirgin hagu da awo 15,a harbe takitin na kusa." Jirgin ruwan yaki mai lamba Liangyungan ya harbe takitin bisa umurnin da aka bayar..nan da nan an samu labarin nutsewar takitin na kusa dake bisa teku.sai sojojin ruwa na kasar Sin suka sanar da takwarorinsu na Britaniya wadanda suka dauki nauyin yin aikin nan ba tare da bata lokaci ba. "Jirgin Sutherland!Jirgin Sutherland! Jirgin Liangyungang ke magana,An nutsar da takitocin guda biyu da aka kafa bisa teku." Mallam Faisal,dan kallo na rundunar soja ta ketare dake jirgin Liangyungang na Sin ya buga taken yabo ga sojojin ruwan Sin.Ya ce "Da kyaun kwarai da gaske,wannan ya burge ni sosai.An nutsar da dukkan takitocin dake bisa tekun,babban aikin bajinta ne da sojojin ruwan kasar Sin suka yi.

Bisa shirin da aka tsara cikin rawar dajin,a yammancin ran 9 ga wata,sojojin ruwan kasar Sin sun dauki nauyin wani aikin ceto cikin hadin kai a teku.Wannan karo ne na farko da sojojin ruwan kasar Sin suka kitsa da umurta aikin ceto na hadin kan kasashe da dama bisa teku.A cikin rawar dajin,'yan jirgi guda biyu na jabu sun fadi cikin teku,jirgin ruwan Liangyungang ya ba da umurnin samame wadanda suka fadi cikin tekun. "Ku mai da hankali,ku mai da hankali !nan jirgin ruwa mai ba da umurni ke magana.ku shirya ku fara aiki ! "jirgin Babl ya samo labarin","jirgin Umar ya samo labarin","jirgin sanmin ya samo",jirgin howes ya samo".

Bayan rabin awa,jirgin ruwan yaki Umar na kasar Bangaladesh ya gano takiti na farko,a cikin 'yan mintuna kadan jirgin yaki na Pakistan ya gano takiti na biyu.Jiragen ruwan yaki biyu sun tsamo mutane biy na jabu daga teku bisa umurnin sojojin ruwan kasar Sin.

Bayan da aka kammala aikin ceto,hafsa hafsoshin sojojin ruwan Sin dake shiga rawar daji mallam Luo Xianlin,sojojin ruwan Sin sun tsara shirin dalla dalla domin tabbatar da samun cikakkiyar nasara cikin aikin ceto.

"Sojojin ruwa na kasar Sin ne suka tsara daukacin shirin ceto bisa teku.dayake muke da karamar matsala wajen harshe,amma mun yi kokari mun warware shi yadda ya kamata.komai na tafiya daidai,babu matsala wajen sadarwa,sojojin ruwa na dukkan kasashen mahalarta sun kware sun cika ayyukansu da aka dora musu."

Babban kwamanda na sojojin ruwan Sin dake halartar rawar daji Mallam Qiu Yanpeng ya bayyana cewa ta hanyar yin rawar daji,sojojin ruwa na kasar Sin sun kara kwarewarsu wajen yakin adawa da makiyi kan teku.Ya ce Manufarmu ta shiga wannan rawar daji na kasashe da dama,ita ce tinkarar 'yan ta'adda daga teku.mun sane da hanyoyi da dabarun da ake bi a cikin ayyukan hadin kan sojojin ruwa na kasashe da dama bisa teku,mun aiwata da ayyukan da aka dora mana cikin nasara,mun kware a cikin yaki bisa teku,hadin kanmu da takwarorinmu na kasashen ketare ya kara zumuncin dake tsakaninmu,mun cimma burinmu."(Ali)