Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-12 15:57:35    
Kasar Sin za ta yi kokari tare da abokan cinikayya, domin sa kaimi ga samun nasarar shawarwari na Doha

cri
Mr. Bo Xilai, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana a ran 12 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ita ce kasar da ke sa himma domin shiga harkokin ciniki na duniya, wadda take dauke nauyin bisa wuyanta, a matsayinta haka, za ta yi kokari tare da muhimman abokanta na cinikayya, ta yadda shawarwari na zagaye Doha za su samun nasara.

Mr. Bo Xilai ya yi wannan jawabi ne a gun taron manema labaru da aka shirya dangane da taron shekara-shekara na majalisar wakilai ta kasar Sin. Ya nuna cewa, yanzu muhimmiyar matsalar da ake fuskanta a shawarwarin Doha ita ce, a matsayinsu na abokan cinikayya da suka fi girma a duniya, Turai da kasar Amurka ba su yi rangwame wajen batutuwan yawan kudin kwastan, da ba da karfin kudi ga fitar da kayayyakin noma, da dai sauran batutuwan noma.

Mr. Bo Xilai ya ce, ya kamata muhimman abokan cinikayya daban daban na duniya su ba da taimakonsu, domin sa kaimi ga shawarwarin Doha da daddale yarjejeniya ta karshe. Kullum bangaren Sin yana fatan ba da taimako bisa manyan tsare-tsare a cikin shawarwarin da ake yi a tsakanin bangarori da dama. (Bilkisu)