Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-11 18:55:49    
Kasar Sin tana kokarin kare ikon mallakar fasaha

cri
A cikin rahoto kan aikin gwamnatin kasar Sin da firayin minista Wen Jiabao ya gabatar a gun bikin kaddamar da cikakken zama na shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin, Mr. Wen ya bayyana cewa, za a karfafa aikin kare ikon mallakar fasaha. Wasu wakilan jama'a da suke halartar wannan cikakken zama na majalisar dokokin kasar Sin, sun gaya wa wakilanmu cewa, tabbatar da aikin kare ikon mallakar fasaha yana da muhimmanci sosai ga cigaban kasar Sin. Suna kuma bayar da shawarwarin cewa, za a iya kare ikon mallakar fasaha ta hanyar kafa da aiwatar da dokoki tare da kuma kara yin hadin guiwa da kasashen waje.

A cikin rahoto kan aikin gwamnatin kasar Sin da Mr. Wen Jiabao ya bayar, an ce, gwamnatin kasar Sin za ta kara saurin tsara da aiwatar da tsarin kare ikon mallakar fasaha da kuma kyautata tsarin sa kaimi ga yunkurin kirkire-kirkire. Mr. Liu Chuanzhi, wani wakilin jama'a na majalisar dokokin kasar Sin kuma shugaban kamfanin Legend Holdings Ltd ya yaba wa kokarin kare ikon mallakar fasaha da gwamnatin kasar Sin take yi. Ya ce, "Kare ikon mallakar fasaha, wannan yana da muhimmanci kwarai da gaske ga kasar Sin. Game da wannan ma'ana, ba ma kawai gwamnati da kamfanoni har da jama'a fararrun hula suna ganewa a kai ba, har ma suna sanin irin wannan muhimmanci da kansu."

Kamfanin Legend Holdings Ltd kamfanin kera injuna masu kwakwalwa mafi girma ne a kasar Sin. A watan Afrilu na shekarar 2006, wannan kamfani da kamfanin Microsoft na kasar Amurka sun daddale wata yarjejeniyar da darajarta ta kai dalar Amurka biliyan 1.2. Bisa wannan yarjejeniya, an fara sanya manhaja mai suna "Windows" na kamfanin Microsoft a cikin injuna masu kwakwalwa na kamfanin Legend Holdings Ltd. Sannan kuma, bayan rabin shekara kawai, an kafa kawancen kare ikon mallakar fasaha ta kamfanonin kasar Sin mai zaman kansa a birnin Beijing. Kamfanonin kasar Sin ne suka kafa ta da kansu domin fama da laifuffukan satar ikon mallakar fasaha.

Mr. Tang Jun, shugaban kamfanin Snda, kuma yana daya daga cikin mutane wadanda suka bayar da shawarar kafa wannan kawance ya bayyana har sau da yawa, cewar ya ga makomar kamfaninsa sakamakon kokarin kare ikon mallakar fasaha da kasar Sin ke yi. Mr. Tang ya ce, "Ko kamfanin Microsoft, ko kamfanin Snda, dukkanmu muna samun moriya domin kokarin kare ikon mallakar fasaha da ake yi. Idan an kwatanta kokarin da ake bayar yanzu da na shekaru 10 ko shekaru 5 ko shekaru 3 da suka wuce, muna ganin makomarmu mai kyau sakamakon kokarin kare ikon mallakar fasaha da ake bayar yanzu a kasar Sin. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, kamfanin Snda ya zama daya daga cikin kamfanonin shafin Internet da suke samun moriya sosai sakamakon kokarin kare ikon mallakar fasaha da ake yi."

Kamfanin Snda wani kamfani ne na shafin internet ya yi suna sosai a kasar Sin. Wannan kamfani ya kirkiro manhajan wasanni iri iri da ake wasa da su a kan shafin internet.

Mr. Liu Fengming, mataimakin babban direktan sashen kasar Sin na kamfanin Microsoft ya kuma yaba wa kokarin kare ikon mallakar fasaha da kasar Sin ke yi. Mr. Liu ya ce, "Kasar Sin tana aiwatar da jerin dokoki da ka'idoji domin kare da kuma yin yaki da satar ikon mallakar fasaha. Wadannan dokoki da ka'idoji suna amfanawa cigaban sana'ar manhaja da kamfanonin kasar Sin suke yi. Sannan kuma suna da muhimmanci sosai ga yunkurin kyautata odar kasuwanci da ta tattalin arziki da kuma sa kaimi ga kara cigaban sana'ar manhaja a kasar."

Lokacin da yake ganawa da wakilinmu, wakilin jama'a kuma shugaban hukumar kare hakkin mai wallafa littafi ta kasar Sin Mr. Long Xinmin ya jaddada cewa, za a kara kare hakkin mai wallafa littafi. "Za a kara kyautata aikin kafa dokokin kare hakkin mai wallafa littafi da aiwatar da irin wadannan dokoki. Game da wasu matsalolin satar ikon mallakar fasaha da suka fi jawo hankulan mutane, za a kara yin bincike a kansu. Ba ma kawai za mu kare karfin kirkire-kirkire namu ba, har ma za mu kare ikon mallakar fasaha na mutanen kasar waje." (Sanusi Chen)