Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-11 17:58:19    
Kasar Sin za ta kara sa ido kan ayyukan kasafin kudi da tattalin arziki a bana

cri
Ran 11 ga wata, a nan Beijing, shugaba Wu Bangguo na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, zaunannen kwamitin zai kara sa ido kan ayyukan kasafin kudi da tattalin arziki a shekarar da muke ciki, zai kuma kara sa ido da yin bincike kan halin da ake ciki a fannin tafiyar da tattalin arziki.

Mr. Wu ya kara da cewa, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin zai dora muhommanci kan sa ido kan halin da ake ciki a fannin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru 5 da aka gabatar a shekarar bara, da daukaka saurin ci gaban tattalin arzikin jama'a yadda ya kamata. A sa'i daya kuma, zai sa kaimi kan bangarorin da abin ya shafa da su sami daidaito a tsakanin kasafin kudin shiga da na kashewa, da yin amfani da rarar kasafin kudin shiga yadda ya kamata da kuma kara kula da rarar basusukan gwamnatin, sa'an nan kuma, zai goyi bayan hukumomin duddubawa da su yi ayyukan dudduba bisa dokoki, da sa kaimi kan bangarorin da abin ya shafa da su shawo kan batutuwan da aka tono.(Tasallah)