Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-11 17:57:30    
Dole ne a kafa dokoki ta hanyar kimiyya da demokuradiyya, a cewar Wu Bangguo

cri

A ran 11 ga wata, a nan birnin Beijing, Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar dokoki ta kasar Sin wato NPC ya bayyana cewa, kafa dokoki ta hanyar kimiyya da kuma demokuradiyya wata bukata ce wajen kyautata ingancin kafa dokoki, shi ya sa dole ne a kafa dokoki bisa wadannan ka'idoji biyu.

A ran nan, an saurari rahoton aiki da Wu Bangguo ya yi a gun taron shekara shekara na NPC, inda Mr. Wu ya bayyana cewa, a shekarar da muke ciki, zaunannen kwamitin zai ci gaba da kyautata ayyukan kafa dokoki a fannin tattalin arziki, a waje daya kuma zai sa kaimi ga kafa dokoki a fannin zamantakewar al'umma.

Haka kuma Mr. Wu ya jaddada cewa, domin dokokin da ake tsara za su iya bayyana ra'ayoyin fararen hula, kuma za a iya tafiyar da su kamar yadda ya kamata, shi ya sa lokacin da ake neman samun ra'ayoyi a rubuce, dole ne a saurari ra'ayoyi na bangarori daban daban kai tsaye. Kuma game da muhimman shirye-shiryen dokoki da ke da nasaba da moriyar fararen hula, ya kamata a sanar da su ga jama'a a fili. Haka kuma game da batutuwan da aka yi gardama da su sosai a cikin shirye-shiryen dokoki, ya kamata a kira tarurukan sauraran abubuwan shaida don yin nazari a kansu.(Kande Gao)