A ran 10 ga wata da dare, Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da sauran shugabannin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma na gwamnatin kasar da wakilan kananan kabilun kasar Sin da ke halartar taron shekara-shekara na majalisar dokoki ta kasar Sin da kuma na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin sun taru a babban dakin taro na jama'ar Beijing domin tayar murnar kira wadannan manyan taruruka biyu cikin nasara.
Shugaba Hu ya yi tadi tare da wakilan kabilun Uygur da Tibet da ke zauna dab da shi, inda ya nuna kulawa sosai kan bunkasuwar wurin da kuma zaman rayuwar fararen hula na wurin.
Haka kuma Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin da sauran shugabannin kasar Sin sun yi tadi tare da wakilan kananan kabilun Sin, inda suka karfafa zukatansu wajen sauke nauyin da aka dora musu kamar yadda ya kamata, da bayyana buri da bukatun fararen hula na kabilu daban daban domin bayar da gudummowa ga kira manyan taruruka biyu cikin nasara.(Kande Gao)
|