Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-11 17:29:13    
Kasar Sin za ta kafa ma'aunin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyuka a bana

cri
Kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ruwaito mana labari a ran 10 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayyana cewa da cewa, a shekarar nan da muke ciki, kasar Sin za ta kafa ma'aunin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyuka daga duk fannoni, cikin himmma da kwazo ne za ta yi kokarin neman kafa tsarin inshora don tsofaffi a kauyukanta.

Ana yi babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka saba shiryawa sau daya a ko wace shekara a nan Beijing. A lokacin da yake tattaunawa tare da wakilan jama'a da suka zo daga jihar Guangxi ta kasar a ran 9 ga wata, shugaba Hu ya mai da hankalinsa sosai kan batutuwan manoma da kauyuka da kuma aikin gona. Ya ce, a shekarun baya da suka wuce, gwamnatin Sin ta fito da manufofi da matakai a jere don goyon baya da ba da gatanci ga manoma. A galibi dai halin da ake ciki a kauyukan Sin na da kyau a shekarun nan da suka wuce. Amma ya zuwa yanzu dai yana kasancewa da abubuwan da aka gaza yi wajen tushen aikin gona, kuma manoma suna fuskantar matsaloli wajen kara samun kudi.

Shugaba Hu ya ci gaba da cewa, a shekarar bana, kasar Sin za ta kafa ma'aunin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyuka daga duk fannoni, da farko dai wannan ma'auni ba zai yi da yawa ba, amma saboda bunkasuwar tattalin arziki da kuma kara zuba kudade, kasar Sin za ta dauki matakan daga ma'aunin nan.(Tasallah)