Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-09 17:39:36    
Kasar Sin tana gudanar da tsarin tattalin arziki da kudin haraji da harkokin kudi yadda ya kamata

cri

A ran 9 ga wata a birnin Beijing, ministan kudi na kasar Sin Jin Renqing ya bayyana cewa, karuwar kudin shiga da gwamnatin kasar Sin ta samu ya zo daga bunkasuwar tattalin arziki da karuwar kwarewar kasar Sin wajen buga haraji, kasar Sin tana gudanar da tsarin tattalin arziki da kudin haraji da harkokin kudi yadda ya kamata.

Mr Jin ya yi wannan bayani ne a gun taron manema labaru na taron shekara shekara na wakilan jama'ar kasar Sin, wanda aka shirya a ran nan a birnin Beijing. Mr Jin ya ci gaba da cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, yawan kudin shiga da gwamnatin kasar Sin ta samu ya karu sosai. Wannan yana da nasaba da fasahohin zamani da hukumomin haraji da kwastan suke amfani da su da kuma kokarin da suke yi wajen karfafa kwarewar ma'aikatansu. Lallai dukkan wadannan matakan da aka dauka sun kara karfafa kwarewar hukumomin haraji.(Danladi)