Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-09 17:35:57    
Taron Majalisar wakilan Jama'ar Sin ya fara dudduba shirirn sabuwar dokar buga haraji kan kudin riba na masana'antu

cri
Ran 8 ga wata, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta gabatar wa taron shekarar nan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da shirin sabuwar doka kan yawan haraji da ake bugawa kan kudin riba na masana'antu don dudduba ta. Bisa sabuwar dokar, za a canja tsarin haraji da ake bugawa a yanzu, za a buga yawan haraji bai daya a kan kudin riba da masana'antun gida da na waje ke samu a kasar Sin, don samar da kyawawan gurabe ga masana'antu da su yi takara a kasuwanni cikin daidaici.

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa a karshen shekarun 1970, ta tsara manufofin yawan haraji ba iri daya da take bugawa a kan masana'antu masu jarin waje da na gida, don jawo jari daga kasashen waje, da bunkasa tattalin arziki. Bisa tsarin buga haraji da ake aiwatarwa yanzu a kasar Sin, ko da yake matsakaicin yawan haraji da ake bugawa a kan kudin riba na masana'antu masu jarin waje da na gida ya kai kashi 33 cikin dari, amma a hakika dai, yawan harajin nan da ake bugawa a kan masana'antun gida ya zarce kashi 10 cikin dari bisa na masana'antu da aka kafa bisa jarin kasashen waje.

Yayin da Malam Jin Renqing, ministan kudi na kasar Sin ke yin bayani kan shirin sabuwar dokar nan ga wakilai mahalartan taron majalisar, ya nuna cewa, "bayan da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO, kasar ta kara bude kasuwanninta ga 'yan kasuwa na kasashen waje, masana'antu na jarin gida ma sun kara shiga cikin tsarin tattalin arzikin duniya sannu a hankali, don haka matsi da ake yi musu wajen yin takarar kullum sai kara tsananta yake yi. Idan kasar ta ci gaba da bin tsoffin manufofin, to, tabbas ne, masana'antu masu jarin gida za su yi takara cikin rashin daidaici, kuma za ta kawo tasiri ga samar da kyawawan gurabe ga takarar da ake yi a kasuwanni cikin rshin daidaici."

Malam Jin Renqing ya kara da cewa, bisa gwargwadon manufofi da ake bi a duniya, shirin sabuwar dokar za ta buga yawan haraji bai daya a kan kudin shiga na masana'antun masu jarin gida da na waje, wato zai kai kashi 25 cikin dari. Ya ce, "shirin sabuwar dokar ta tsai da yawan haraji da za a bugawa a kan kudin shiga na masana'antun masu jarin gida da na waje ya kai kashi 25 cikin dari. Manyan abubuwa da aka yi la'akari da su, su ne ya kamata, a rage yawan haraji da ake bugawa a kan masana'antu masu jarin gida, sa'an nan kuma yawan haraji da za a buga a kan masana'antu masu jarin waje zai karu kadan kamar yadda ya kamata. Ka zalika ya kamata, a yi la'akari da yawan irin wannan haraji da ake bugawa a duniya musamman kasashe da ke makwabtaka da kasar Sin. Kashi 25 cikin dari na harajin ba su yi yawa ba, idan an kwatanta su da na kasashen waje, don haka za a kawo amfani ga masana'antun wajen daga matsayinsu na yin takara a kasuwanni, kuma a jawo kudin jari daga 'yan kasuwa na kasashen waje."

Malam Jin Renqing ya ci gaba da cewa, yin haka ba zai kawo babban tasiri ga aikin samar da kayayyaki da masana'antu masu jarin waje ke yi a kasar Sin ba. Ya bayyana cewa, "bisa abubuwa da aka tanada a cikin wannan sabuwar doka, za a ci gaba da nuna gatanci wajen buga haraji kan wasu masana'antu masu jarin waje kamar masana'antu na sabuwar fasaha da masana'antu masu cin riba kadan, haka kuma za a aiwatar da manufofin nuna gatanci wajen buga haraji kan sauran masana'antu masu jarin waje a lokacin wucin gadi, bayan aiwatar da sabuwar dokar nan, ba za a kawo babban tasiri ga harkokin samar da kayayyaki da masana'antu masu jarin waje ke yi ba. " (Halilu)