Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-09 17:01:43    
Majalisar gudanarwar kasar Sin za ta kafa kamfanin zuba jari na kudin musanya

cri

Ran 9 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Jin Renqing ministan sha'anin kudi na kasar Sin ya ce, majalisar gudanarwar kasar Sin za ta kafa kamfanin zuba jari na kudin musanya, don kara cin gajiya daga harkokin kudin musanya.

Mr. Jin Renqing ya sanar da wannan labari a gun taron manema labaru na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. Ya ce, hukumar kula da kudin musanya ta kasar za ta cigaba da sarrafa da kudadden musanya da kasar ta tanada yadda ya kamata. Amma wannan kamfanin zuba jari na kudin musanya da ke karkashin jagorancin majalisar gudanarwa zai kula da harkokin zuba jari na kudan musanya, zai yi iyakacin kokarinsa don kara cin gajiya daga harkokin kudin musanya. Yanzu ana shirya kafuwar wannan kamfani.