Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-09 15:49:55    
Labarai game da wasannin Olympic

cri

Aminai makaunata, ko kuna sane da, cewa alkalan wasa suna kan matsayi mai muhimmanci a gun taron wasannin motsa jiki na Olympic na can can zamanin da.

Lallai alkalan wasa na taron wasannin Olympic na can can zamanin da suna da babbar hujja, wadanda sukan sa babbar riga mai launin shuni kuma sanye da hular fure a ka, wadda aka kirkiro da reshen itacen Olive yayin da suke rike da bulala a hannu wadda ke alamanta ikon mulki. Alkalan wasa sukan yi amfani da irin wannan bulala domin buga 'yan wasa wadanda suka karya dokokin wasa.

Idan aka kwatanta alkalan wasa na zamanin yau, to ana iya ganin, cewa alkawalan wasa na can can zamanin da suna da hujjoji da dama. Tuni wata daya kafin a gudanar da taron wasannin Olympic, akan tura 'yan wasa zuwa wani wurin dake kusa da inda ake gudanar da taron wasannin Olympic domin koyon ka'idoji kan harkokin gasanni; A sa'I daya kuma, alkalan wasa sukan sa ido kan iznin da 'yan wasa suke da shi ta hanyoyi daban daban yayin da suke fadakar da su kan abubuwan da ya kamata su mai da hankali a kai a duk tsawon lokacin gasanni. A karshe dai, alkalan wasa sun zabi 'yan wasan da suke da iznin shiga gasanni

Wani abu mai sha'awa shi ne, an dora babban nauyi bisa wuyan alkalan wasa a gun taron wasannin Olympic na can can zamanin da, wato kafin a bude taron wasannin Olympic, alkalan wasa suka mika umurnin dakatar da yin yaki zuwa garuruwa daban daban na kasar Girka. Wannan dai wani mhimmmin dalili ne da ya sa aka nace ga gudanar da taron wasannin Olympic na can can zamanin da sau daya cikin shekaru hudu. Rahoton tarihi ya yi nuni da ,cewa kafin a gudanar da taron wasannin Olympic, alkalan wasa sukan hawa kan dawaki rike da wutar yula mai tsarki da aka samo daga kan tsauni mai tsarki na Olympia zuwa garuruwa daban daban na Girka domin ba da umurnin dakatar da yin yaki. Nan take aka dakatar da yin yaki sa'annan aka bude dukkan hanyoyi wadanda aka rufe a lokacin yaki. To, bayan da aka aiwatar da umurnin daina yin yaki, sai nan da nan mutane suka bi wadanan hanyoyi zuwa wurin da ake gudanar da taron wasannin Olympic. Daga nan, ana ganin, cewa dalilin da ya sa taron wasannin Olympic na can can zamanin da ya dade har na tsawon shekaru fiye da dubu daya, shi ne alkalan wasa suka ba da umurnin dakatar da yin yaki kafin a gudanar da taron wasannin Olympic na can can zamanin da.

Wasu hujjoji na alkalan wasa na taron wasannin Olympic na can can zamanin da, sun hada da jan ragamar tawagar wakilan 'yan wasa zuwa haikalin tsafi na sararin samaniya domin yin rantsuwa, da shirya harkokin gasanni, da zaben wadanda suka cimma nasara da kuma yanke hukunci a fannin wasa. To, a bayyane ne aka gano, cewa a cikin wadannan hujjoji, hujjar yanke hukunci a fannin wasa ce kacal alkalan wasa na yanzu suke da ita.

Jama'a masu saurare, an iske wani abun mamaki, cewa a cikin shekaru 200 na farkon taron wasannin Olympic na can can zamanin da, alkalin wasa daya kadai aka samu, shi ne sarkin kasar Girka. Daga baya, wato a cikin shekaru fiye da 1,000 na tarihin tarurrukan wasannin Olympic na can can zamanin da, 'yan iyalin garin Elis ne suka yi gadon daukar nauyin alkalan wasa, wato ke nan 'yan kabilu daban daban dake zama cikin garin Elis sukan zabi mutane biyu don su zama alkalan wasa. Ya zuwa shekara ta 480 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisalam, yawan 'yan alkalan wasa ya karu zuwa 9, kuma kowane daga cikinsu yana da nasa aiki; A tun taron wasannin Olympic na 108 na can can zamanin da da aka yi a shekarar 384 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisalam, yawan alkalan wasa ya karu zuwa 10.

To, yaya ne ake iya ba da tabbaci ga yanke hukunci bisa matsayin daidaici da alkalan wasa daga wani gari daya tak suke yi ga 'yan wasa na sauran garuruwa? Akan dauki jerin matakai a gun taron wasannin Olympic na can can zamanin da domin tabbatar da yin gasanni bisa matsayin adalci. Daya daga cikin matakan, shi ne yin bikin rantsuwa. Lallai irin wannan biki yana da muhimmancin gaske ga gudanar da taron wasannin Olympic na can can zamanin da.

A gun bikin rantsuwar, alkalan wasa sun lashi takobin rashin cin hanci da rashawa yayin da suke daukar nauyin dake bisa wuyansu. Lallai halin rashin son zuciya da alkalan wasa suka nuna ya samu amincewa daga 'yan kallon wasa. Ko da yake akan samo wasu 'yan wasa da suka zama zakara a gun taron wasannin Olympic daga cikin 'yan iyalansu, amma mutane ba su taba yin shakkar cewa 'yan wasan suka yi magudi a gun gasa ba.

Idan akwai wasu mutane da suka nuna bambancin ra'ayi ga sakamakon hukuncin da alkalan wasa suka yanke, to za su iya daukaka kara. Idan an tabbatar da cewa hukuncin da alkalan wasa suka yanke na kuskure ne, to za a yanke musu hukunci mai tsanani. Yanzu ma haka ake yi lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na zamanin yau.( Sani Wang )