Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-09 15:31:13    
Sabuwar dokar harajin da aka buga bisa kudin shiga da kamfanonin suka samu ba zai yi illa ga kamfanonin HongKong da Macao da kuma Taiwan ba

cri
Ministan kudi na kasar Sin Jin Renqing ya yi bayani a ran 9 ga wata a birnin Beijing, cewa sabuwar dokar harajin da aka buga bisa kudin shiga da kamfanonin suka samu ba zai yi illa ga kamfanonin HongKong da Macao da kuma Taiwan ba.

Mr. Jin ya yi wannan bayani ne lokacin da yake amsa tambayar da wani dan jarida na Taiwan ya yi masa a ran nan a gun taron manema labarai na taron shekara-shekara na majalisar dokoki ta kasar Sin. Kuma ya kara da cewa, a cikin shirin sabuwar dokar harajin da aka buga bisa kudin shiga da kamfanonin suka samu, an buga harajin iri daya ga kamfanonin kasar Sin ciki har da na HongKong da Macao da kuma na Taiwan. Amma a waje daya kuma an kiyaye yawan harajin ba da gatanci da aka buga ga wasu sana'o'i, shi ya sa kamfanonin HongKong da Macao da kuma Taiwan da ke tafiyar da ayyukansu na wadannan sana'o'i za su iya samun irin wannan harajin ba da gatanci da aka buga.(Kande Gao)