Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 20:51:00    
Babban yankin kasar Sin ba zai yarda da ko wane mutumin da ya raba Taiwan daga kasar Sin ta ko wace hanya ba

cri

A halin yanzu, ana kan gudanar da babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato hukumar koli ta kasar a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin. A ran 8 ga wata, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya tattauna da tawagar Taiwan, inda ya ce, ko kusa babban yankin kasar Sin ba zai yarda ko wane mutum ya raba Taiwan daga kasar Sin ta ko wace hanya ba.

Mr Jia ya ce, a cikin shekarar da ta shige, babban yankin kasar Sin yana tsayawa tsayin daka a kan babban take na bunkasa dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan cikin zaman lafiya, ta haka ya kiyaye zaman karko na dangantakarsu. Amma mahukuntan Taiwan sun nuna taurin kai wajen bin tsatsaurar akidar neman 'yancin Taiwan, kuma sun nemi samun 'yancin Taiwan bisa doka ta hanyar yin gyara a kan tsarin mulkinta. A 'yan kwanakin baya, shugabannin mahukuntan Taiwan sun gabatar da ra'ayin neman 'yancin Taiwan, wannan ya zama wani mataki daban da suka dauka, wanda ke iya haifar da hadari.(Danladi)