Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 20:19:28    
An gabatar da daftarin dokar mallakar dukiyoyi ga taron NPC

cri
A yau 8 ga wata, a hukunce ne aka gabatar da daftarin dokar mallakar dukiyoyi ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato majalisar NPC, wadda kuma ta kasance hukumar koli ta kasar. Kafin wannan kuma, zaunannen kwamitinta ya riga ya duba daftarin dokar har sau bakwai. Daftarin dokar dai ya bi tsarin tattalin arzikin kasar Sin mai tushe, kuma ya nemi da a kare dukiyoyin gwamnati da na jama'a da kuma na mutane masu zaman kansu cikin daidaici.

Yau, a yayin da mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Mr.Wang Zhaoguo ke yin bayani a kan daftarin dokar a gaban wakilan majalisar NPC kusan 3000, ya ce, wannan muhimmiyar doka ce da ke kasancewa tamkar ginshiki a cikin tsarin dokokin kasar Sin.

An ce, an fara tsara dokar mallakar dukiyoyi ne tun daga shekarar 1993, kuma bayan da aka shafe shekaru 9 ana tsara dokar, an kama hanyar kafa dokar. Mr.Wang Zhaoguo, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya ce, ana bin ka'idoji hudu ne a wajen kafa dokar nan ta mallakar dukiyoyi. Ya ce, "Bisa hakikanin halin da kasar Sin ke ciki, mun bayyana tsarin tattalin arziki mai tushe yadda ya kamata daga dukan fannoni da kuma tsayawa tsayin daka a kansa. Sa'an nan, bisa tsarin mulki da kuma dokoki, za a aiwatar da ka'idar kare dukiyoyin gwamnati da na jama'a da kuma na mutane masu zaman kansu cikin daidaici, kuma game da matsalar hasarar dukiyoyin gwamnati, za mu kara kare dukiyoyin gwamnati. Bayan haka, za mu bayyana manyan manufofin da ke shafar kauyuka yadda ya kamata kuma daga dukan fannoni, tare da kuma kare moriyar manoma. Daga karshe kuma, game da batutuwan da ke matukar bukatar kayyadewa, za mu daidaita moriyar bangarori daban daban, don sa kaimin samun jituwar al'umma."

A matsayinta na kasar da ke da tsarin mallakar gwamnati a matsayin babban tsarin tattalin arzikinta, yadda kasar Sin za ta kare dukiyoyin gwamnati da na mutane masu zaman kansu, wannan ya taba zama babban abin da ya fi jawo hankulan jama'ar gida da na waje a kan daftarin dokar mallakar dukiyoyi. Mr.Wang Zhaoguo ya ce, "A yayin da aka tabbatar da wa ke da hakkin mallakar dukiyoyi, ko gwamnati ko jama'a ko kuma mutane masu zaman kansu, ya kamata a kare hakkinsu na mallakar dukiyoyi cikin daidaici. Amma kare su cikin daidaici ba ya nufin wai dukan tsarurrukan tattalin arziki suna zaman daidaici a cikin tattalin arzikin kasa. A'a, ba haka ba, a muhimman sana'o'i da fannoni da ke shafar tsaron kasa da tattalin arzikin kasa, tilas ne a danka su a karkashin mallakar gwamnati, kuma dokar tattalin arziki da ta mulki ne ke kayyade su."

Bisa daftarin dokar, ba ma kawai dokar za ta kare kudin shiga da gidaje da kuma kayayyakin masarufi na mutane masu zaman kansu ba, haka kuma za ta kare kudadensu na ajiya da zuba jari da suka yi da kuma ribar da suka ci, kuma za ta hana ko waye kwashe dukiyoyin mutane masu zaman kansu ko kuma lahanta su. Mr.Wang Zhaoguo ya kuma yi bayani a kan dalilin da ya sa aka tsara wadannan ka'idoji, ya ce, "Bayan da aka aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa cikin sauri, kuma an yi ta kyautata zaman rayuwar jama'a, dukuyoyin da ke karkashin mallakar mutane masu zaman kansu ma sai kara karuwa suke yi a kullum. Kare dukiyoyin mutane masu zaman kansu yadda ya kamata, ba ma kawai abu ne da aka tsara cikin tsarin mulki ba, haka kuma abu ne da jama'a ke matukar bukata. Ka'idojin sun kara kyautata tsarin dokokin kasar Sin a fannin kare dukiyoyin mutane masu zaman kansu, haka kuma za su taimaka wajen sa kaimi ga jama'a da su yi kokarin kawo albarka da kuma sa kaimin samun jituwar al'umma."(Lubabatu)