Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 18:49:26    
Jihar Tibet tana kara samun kyautattuwa da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba

cri

A ran 8 ga wata a birnin Beijing, shugaban jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin Qiangba Puncog ya bayyana cewa, a halin yanzu, jihar Tibet tana kara samun kyautattuwa da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba.

Qiangba Puncog ya yi wannan bayani ne a yayin da tawagar Tibet take amsa tambayoyin da manema labaru suke mata, wadda take halartar taron shekara shekara na wakilan jama'ar kasar Sin. Qiangba Puncog ya ce, bara ta zama babbar shekara da jihar Tibet ta fi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan karuwar tattalin arzikinta ya kai kashi 13.4 bisa dari. Kudin shiga da manoma da makiyayya suka samu ya kara karuwa sosai, kuma an kara kyautata zaman rayuwarsu da yanayin aikinsu. Haka kuma an samu saurin bunkasuwar tattalin arziki mai zaman kai, yawan kayayyakin da mazauna birane da manoma suka anmfani da su ya karu sosai.

Qiangba Puncog ya ci gaba da cewa, a cikin shekarar da muke ciki, jihar Tibet za ta kara samun kyakkyawar dama kamar hanyar jiragen kasa na Qinghai da Tibet da dai sauransu domin samun bunkasuwa mai jituwa da kara jin dadin jama'ar jihar Tibet.(Danladi)