Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 18:21:48    
A hakika, makasudin babban yankin Tibet da Dalai Lama ya gabatar shi ne don neman 'yancin kai

cri
Ran 8 ga wata, a nan birnin Beijing, Malam Qiangba Puncog, shugaban hukumar jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin ya bayyana cewa, Dalai Lama ya gabatar da babban yankin Tibet mai ikon kai da cin kashin kansa sosai, ainihin makasudinsa shi ne don neman 'yancin kai ta hanyar haifar da tasiri ga kafofin watsa labaru na duniya.

A yayin da Qiangba Puncog ke karbar ziyarar da maneman labaru na gida da waje suka yi masa a wannan rana a birnin Beijing, ya ce, game da batun wai babban yankin Tibet, ba a taba kafa wani babban yankin Tibet mai dinkuwa a fannin siyasa ba, tun bayan da aka hamburar da daular Tufan a karni na 9. Yanzu, Dalai Lama ya jirkitar da hakikanan abubuwa da ra'ayoyi, ya harhada mulkin siyasa daban daban da ba a taba samu ba a gu daya don rude hankulan mutane da ba su san hakikanan abubuwa da tarihin kasar Sin ba a duniya.

Bayan haka Qiangba Puncog ya kara da cewa, gwamnatin Sin ta nuna matsayinta a fili, ta nemi Dalai Lama da ya yi watsi da ra'ayinsa kan 'ynacin kan Tibet kwata kwata, ta amince da cewa, tun can can da, Tibet wani yanki ne da ba a iya balle shi ga yankun kasar Sin ba, kuma Taiwan ma wani yanki ne na kasar Sin. Abin da ya fi muhimmanci, shi ne, a gaskiya, ya daina yin harkokinsa na wai neman 'yan kan Tibet. (Halilu)