Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 17:30:43    
Babban taron NPC ya soma dudduba shirin kuduri dangane da yawan sabbin 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da kuma batun yin zaben

cri
Yau ranar 8 ga wata, an gabatar da shirin kuduri dangane da yawan sabbin 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da kuma batun zaben ga babban taron majalisar, don dudduba shi. Shirin kudurin ya tsaida cewa, a cikin sabbin wakilan jama'ar kasar da za a zaba a watan Janairu na shekara mai zuwa, yawan mata, da ma'aikata, da kuma manoma zai karu.

Mataimakin shugaban zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sheng Huaren ya yi bayani kan wannan ga taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato NPC da ake yi a nan birnin Beijing. Ya ce, shirin kudurin ya kayyade cewa, yawan wakilai mata na sabon karo zai kai fiye da kashi 22 cikin dari, daga kashi 20 cikin dari na wannan karo; yawan wakilan da suka fito daga ma'aikata da manoma zai fi yawa bisa na wannan karo; bayan haka kuma, ya kamata akwai wakilan ma'aikata 'yan ci-rani, wadanda suka fito daga jihohi da biranen da ma'aikatan da yawa ke taru. (Bilkisu)