Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 16:27:15    
An gabatar da shirin dokar buga haraji kan kudin shiga na masana'antu ga taron MWJ ta Sin don bincikenta

cri
Ran 8 ga wata, an gabatar da shirin dokar buga haraji kan kudin shiga da masana'antu ke samu ga taron shekara-shekara da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ke yi a nan birnin Beijing. Bisa shirin dokar, an yi shrin buga yawan haraji bai daya a kan duk masana'antun gida da waje a kasar Sin, don samar da kyawawan gurabe ga masana'antu iri daban daban su yi takararsu a kasuwanni cikin daidaici.

A halin yanzu, yawan haraji da ake bugawa a kan kudin shiga na masana'antun gida da na waje ya kai kashi 33 cikin dari a kasar Sin. Amma yawan harajin da ake bugawa a kan kudin shiga na wasu masana'antun musamman masu jarin kasashen waje ya kai kashi 15 zuwa 24 cikin dari kawai. Bisa kidayar da aka yi, an ce, a hakika dai, yawan haraji da ake bugawa a kan masana'antun gida ya wuce na masana'antun masu jarin kasashen waje misalin kashi 10 cikin dari.

A gun taron shekara-shekarar da majalisar ta yi a ran 8 ga wata, Malam Jing Renqing, ministan kudi na kasar Sin ya bayyana cewa, yin kwaskwari kan harajin kudi da ake bugawa a kan kudin shiga na masana'antu ra'ayi daya ne ga bangarori daban daban na kasar Sin. (Halilu)