Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-08 14:11:03    
Za a ci gaba da yin shawarwari tsakanin Japan da Korea ta Arewa domin mayar da dangantaka a tsakaninsu yadda ya kamata

cri

A ran 7 ga wata da dare, wani jami'in ofishin jakadancin Korea ta Arewa da ke Vietnam ya bayyana cewa, Bayan daidaicin da aka samu, Korea ta Arewa da Japan sun yarda da cewa, daga ran 8 ga wata a birnin Hanoi, hedkwatar kasar Vietnam, za a ci gaba da yin shawarwari tsakanin Japan da Korea ta Arewa domin mayar da dangantaka a tsakaninsu yadda ya kamata. Daga bisani kuma ofishin jakadancin Japan da ke Vietnam shi ma ya tabbatar da wannan labari.

Bisa "Sanarwar hadin gwiwa" da aka zartas a gun taron mataki na 3 na shawarari na zagaye na 5 da aka yi a watan Fabrairu na wannan shekara a tsakanin bangarori 6, an ce, Korea ta Arewa da Japan sun yarda da cewa, za su sake yin shawarwari kan matsalar mayar da dangantaka a tsakaninsu yadda ya kamaya. A ran 7 ga wata da safe a birnin Hanoi na kasar Vietnam, an fara yin taron kungiyar aikin mayar da dangantaka yadda ya kamata a tsakanin Japan da Korea ta Arewa. A gun shawarwarin da aka yi a wannan rana da safe, bangarorin 2 kowanensu ya bayyana matsayinsa na kansa. Mr. Koichi Haraguchi, wakilin Japan kuma jakadan yin shawarwari na kasar Japan ya bayyana cewa, yana fatan bisa tunanin "sanarwar Pyongyang" da aka daddale a shekarar 2002 a tsakanin Japan da Korea ta Arewa, bangarorin 2 za su daidaita matsalar yin garkuwa da mutane da sauran matsaloli gaba daya, ta yadda za a tabbatar da dangantaka a tsakaninsu yadda ya kamata. Mr. Song Il-Ho, wakilin Korea ta Arewa, kuma jakadan shawarwari na bangaren kasar ya bayyana cewa, ya kamata bangarorin 2 su kawar da tarihi mai bacin rai sosai, kuma su daidaita matsalolin da ke tsakaninsu.

A gun shawarwarin, wakilin Japan Mr. Koichi Haraguchi ya nanata cewa, sharadin farko wajen daidaita matsalar mayar da dangantaka tsakanin Japan da Korea ta Arewa yadda ya kamata shi ne daidaita matsalar yin garkuwa da mutane. In da ba a daidaita wannan matsala ba, ba mai yiwuwa ba ne za a mayar da dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 yadda ya kamata, wannan kuwa ka'ida ce ta kullum ta gwamnatin Japan. Amma wakilin Korea ta Arewa ta bayyana cewa, an riga an daidaita matsalar garkuwa da mutane wadda ta faru a tsakanin Korea ta Arewa da Japan, Korea ta Arewa ta riga ta yi duk abubuwan da ya kamata ta yi. Sabo da haka shawarwarin shawarwarin ya tsinke.

An ce, a wannan rana da dare, jami'an kasar Japan sun je wajen ofishin jakadancin Korea ta arewa da ke kasar Vietnam inda suka yi musanyar ra'ayoyinsu da jami'an Korea ta Arewa kan matsalar ci gaba da yin shawarwari, kuma sun samu ra'ayi daya kan wannan matsala, wato bangarorin 2 sun yarda da cewa, a gun shawarwarin da za a yi a tsakaninsu, za su tattauna matsalar biyan diyyar yaki daga Japan da ta yin garkuwa da mutane.

Manazarta sun bayyana cewa, har ila yau ya kasance da wasu cikas kan matsalar mayar da dangantaka tsakanin Korea ta Arewa da Japan yadda ya kamata, daya ita ce matsalar yin garkuwa da mutane, wato mutane 11 na Japan wadanda aka tsare da su zuwa Korea ta Arewa. A watan Satumba na shekarar 2002 a birnin Pyongyang, Mr. Kim Jung-il, shugaban kasar Korea ta Arewa ya yi shawarwari da Mr. Junichiro Koizumi, firayim ministan kasar Japan na wancan lokaci, a gun shawariwarin ya amince da wannan matsalar yin garkuwa da mutane, kuma an mayar da wadannan mutane kasar Japan, amma Japan ta tsaya a kan ra'ayinta cewa, har ila yau da akwai wasu mutanen Japan da aka yi garkuwa da su a kasar Korea ta Arewa. Na 2 kuma ita ce, matsalar diyyar yaki da Japan za ta yi sabo da harin da ta kai wa Korea ta Arewa a tarihi. Amma yanzu sabo da bangarorin 2 dukkansu babu yiwuwar yin rangwame na gaskiya, shi ya sa da akwai doguwar hanyar da za a bi domin mayar da dangantaka a tsakanin Korea ta Arewa da Japan yadda ya kamata.(Umaru)